Kyan tafiya dawowa: Ya dawo addinin musulunci bayan ya yi ridda

Kyan tafiya dawowa: Ya dawo addinin musulunci bayan ya yi ridda

A kwanakin baya ne Legit.ng ta kawo maku labarin wani matsahi, Baba Sabana Afcott, da ya koma addinin Kirista.

Sai kuma ga shi cikin kasa da sati biyu matashin ya dawo addinin musulunci kamar yadda ya sanar da kan sa a shafinsa na sada zumunta, Facebook.

Ga abinda matashin ya rubuta a shafin sa na Facebook, "Jama a barkanmu da warhaka, ni gen.baba sabana afcott yola wanda na fitar da sanarwar cewa na chanja Addini daga addinin musulunchi nakoma addinin Christianity, inda kuma tuni na sanar da dangina hakan, dakuma wasu abokaina.

Kyan tafiya dawowa: Ya dawo addinin musulunci bayan ya yi ridda
Matashi Baba Sabana Afcott

To bayan faruwar hakan ne fa masoya na dakuma dangina duk suka fada cikin bakin ciki kwarai, wasu ma ko abinci basa iya ci a sanadi na, wasu kuka sukayi tayi suna zubar da hawaye saboda kauna ta da sukeyi, wasun kiran lambobin wayoyina suke tayi dare da Rana. Suna tayimini nasiha da kuma rokona akan na yi hakuri na sake tunani akan wannan abu, na sami kiran waya daga jihohin kasar Nigeria daban-daban, sannan ankirani daga kasar Nijar ma, daga kasar chad nasami wani masoyina da ya nuna firgitar sa akan lamarin, nasihohi dai iri iri, kala-kala nayi ta samu daga kowane lungu da sako na duniya, manya manyan mutane masoyana sun kira tare da rokona da in canja shawara, wasun ma har kuka suke tayi, to akwai wan mu da muke uwa daya uba daya dashi, sai yakira ni, yake roko na shima, kamar zaiyi kuka, to saboda wannan irin soyayyar da kuka nuna min, dakuma shawar warinda kukayi ta bani, na yarda na amince, nakoma addinin musulunchi, saboda Allah kuma nakoma, ayanzu dai nakoma addinin Islam kuma, nagodewa duk Wanda ya taimaka da addu'o'i, har Allah kuma ya amsa, kuma kar a damu da cewa za'a taramini wani Abu, ina 'yar sana'a ta, Ina cajin wayoyi, don haka kar kowa yadamu, kuma talauchi baya sakani inbar addini, kudi kuma base sawa a kaura daga wani addin a koma wani, nagode wa masoya na maza da Mata bakida ya.

DUBA WANNAN: Tinubu ya yi magana a kan takarar Buhari, ya yi bayanin matsalar da suke fuskanta

Wannan shine abinda matashin ya rubuta da kan sa a shafin Facebook. Allah kanuna mana gaskiya ka bamu ikon bin ta, ka nuna mana karya sannan ka bamu ikon guje mata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel