Allah ba mai rabo sa’a: Jerin masu takarar kujerar Gwamnan Ekiti a APC

Allah ba mai rabo sa’a: Jerin masu takarar kujerar Gwamnan Ekiti a APC

Mun kawo maku jerin mutanen da ke takarar Gwamnan Jihar Ekiti a karkashin Jam’iyyar APC mai mulki yayin da Gwamna mai-ci Ayodele Fayose ke shirin barin kujerar nan da ‘yan watanni.

Su ma dai ‘Yan Jam’iyyar PDP sun sha alwashin cewa sai sun tika ‘Dan takarar Gwamna Ayo Fayose da kasa a zaben fitar-da-gwani. Ga dai jerin ‘Yan takarar da su ka fito karkashin APC:

Allah ba mai rabo sa’a: Jerin masu takarar kujerar Gwamnan Ekiti a APC

Za ayi yaki wajen karbar kujerar Gwamnan Jihar Ekiti

1. Segun Oni

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Yankin Kudancin Najeriya kuma tsohon Gwamnan Jihar watau Injiniya Oni zai dawo a fafata da shi wannan karo.

2. Kayode Fayemi

Ministan ma’adanai na kasar a yanzu kuma Gwamnan da ya Ayo Fayose wuri watau Dr. Fayemi ya sha alwashin dawowa kan kujerar sa a wannan shekarar.

3. Opeyemi Bamidele

Opeyami Bamidele tsohon ‘Dan Majalisar Tarayya ne da ya wakilici Jihar Ekiti a karkashin Jam’iyyar LP a lokacin yana cikin masu neman Gwamna.

KU KARANTA: Wani babban Lauya yana cikin masu yakin neman zaben Buhari

4. Ayo Arise

Sanata Arise ya taba yin Sanata a Jihar daga 2007 zuwa 2011 a karkashin tutar PDP. Yanzu dai ya dawo APC kuma yace shi ya fi kowa dacewa da Gwamnan Jihar.

5. Femi Bamisele

Tsohon Kakakin Majalisar dokokin Jihar na Ekiti Rt. Hon. Femi Bamisele ya fito takarar Gwamnan Jihar inda yace muradun sa za su tafiyar da Jihar gaba.

6. Victor Kolade

Victor Kolade ya fito takara a Jam’iyyar APC inda yace za a ga aiki idan ya zama Gwamna yana mai kaca-kaca da manufofin Gwamna mai-ci watau Ayo Fayose.

7. Gbenga Aluko

Tsohon Sanatan Jihar a Majalisar 1999 Aluko yana cikin masu harin kujerar Ayo Fayose kuma yace sauran ‘yan takarar ba su ba shi tsoro ko kadan.

8. Babefemi Ojudu

Sanata Ojudu wanda ke cikin masu ba Shugaba Buhari shawara kan harkokin siyasa yana cikin wadanda za su jarraba sa’ar su a zaben Ekiti na wannan shekarar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel