Za'a yiwa wani mutum bulala 80 saboda kirar surukarsa karuwa

Za'a yiwa wani mutum bulala 80 saboda kirar surukarsa karuwa

- Wata kotun musulunci ta yanke wa wani mutum hukunci bulala 80 saboda kirar surukarsa karuwa

- Mutumin ya kira ta karuwa ne sakamakon rashin jituwa da suka samu inda ta kira shi barawo kuma dan kwaya

- Kotu ta bashi damar ya janye maganar amma yaki har ma ya kara da cewa baiyi nadamar abinda ya fadi ba

A ranar Litinin ne wata kotun Shari'ah da ke zaune a Magajin Gari, jihar Kaduna ta hukunta wani Shuaibu Umar ta hanyar yi masa bulala 80 saboda ya kira surukarsa, Suwaiba Abdulkadir karuwa.

Suwaiba ta shigar da kara a kotu ne inda tace kanin mijin nata a kada baki ya kira ta karuwa ne bayan sun sami wata rashin jituwa wanda hakan cin mutunci ne da bata mata suna.

Kotu tayi wa wani bulala 80 saboda ya kira surukarsa karuwa

Kotu tayi wa wani bulala 80 saboda ya kira surukarsa karuwa

DUBA WANNAN: Kotu ta raban auren shekaru 10 saboda tsananin masifar wata mata

"Shuaibu kanin miji na ne kuma sun sami rashin jituwa har ta kai ga cacar baki inda ya kira ni karuwa. "Ina bukatar wannan kotun mai daraja ta bi mani hakki na saboda bata min suna da suruki na yayi," inji ta.

Wanda aka shigar da karar ya amsa cewa tabbas ya kira ta karuwa, kuma ya kara da cewa ya fadi hakan ne cikin bacin rai amma baiyi nadamar fadin hakan ba.

"Raina ya baci lokacin data kirani barawo kuma dan kwaya, shi yasa nima na kirata karuwa kuma ba zan janye abinda na fada ba," inji shi.

Alkalin kotun, Dahiru Lawal ya yanke hukuncin cewa a yiwa Umar bulala 80 bayan an bashi damar janye kazafin amma bai amince ba.

"Wanda ake tuhuma ya amsa cewa ya kira surukarsa karuwa kuma yaki janye maganar daya fada; saboda haka ni Dahiru Lawal, na yanke hukuncin cewa ayi wa Shuaibu bulala 80.

"Hukuncin yayi daidai da koyarwa Annabi Muhammad (SAW) inda yace babu wanda zaiyi wa wani kazafin zina facce ya gabatar da shedu guda hudu wanda suka gani da idanunsu.

"Za'ayi masa bulala 80 saboda cin mutunci da bata sunan wadda ta shigar da kara," inji Alkalin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel