Duk rana sai an fitar da Biliyan 2 domin Boko Haram a mulkin Jonathan – Naja’atu Muhammad
Sai a makon nan mu ke samun labari daga Hajiya Naja’atu Muhammad cewa a duk rana ta Allah a lokacin tsohon Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan yana mulki sai an fitar da Naira Biliyan 2 domin sha’anin tsaro a Najeriya.
Sanata Naja’atu Muhammad tayi wani jawabi kamar yadda mu ka samu rahoto daga Jaridar The Cable a wajen taron tunawa da Yaran Chibok da Boko Haram su ka sace a Abuja inda ta zargi manyan kasar kan rikicin Boko Haram.
Fitacciyar ‘Yar siyasar tace Ali Mode Sheriff yana cikin wadanda su ka hura rikicin Boko Haram domin shi ya dasa su a lokacin yana Gwamna. Muhammad tace tsohon Gwamnan na Borno ya taba nada ‘Dan Boko Haram Kwamishina.
KU KARANTA: Na-kusa da Shugaban kasa Buhari yayi kaca-kaca da shi kan Boko Haram
Tsohuwar Sanatar ta Kanotace Gwamnatin Jonathan tayi amfani da wannan dama ta rika satar dukiyar kasa har Naira biliyan 2 a kowace rana amma ba a ga gyara a harkar tsaro ba. Muhammad tace an maida rikicin hanyar cin kudi a lokacin.
Ita ma dai fitacciyar ‘Yar siyasar tace Gwamnatin Najeriya tayi sakaci wajen kare rayukan jama’a ta kara da cewa babu gidan da rikicin Boko Haram bai shafa ba a Jihar Borno. A karshe ta nemi ayi wa Rundunar Sojin kasar garambawul gaba daya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng