An haifi wani jariri bayan mutuwar iyayen sa da shekaru hudu

An haifi wani jariri bayan mutuwar iyayen sa da shekaru hudu

- Wata kafar yada labarai a kasar China ta ce an haifi wani jariri shekaru hudu bayan mutuwar iyayensa

- Kafar yada labaran ta ce iyayen jaririn sun mutu ne sakamakon wani hatsari da ya ritsa da su

- Bayan haihuwar sa, kakannin sun gudanar da gwajin kwayoyin halitta na DNA kuma sun tabbatar da jaririn jininsu ne

Wata kafar yada labarai a kasar China ta ce an haifi wani jariri shekaru hudu bayan mutuwar iyayensa.

Kafar yada labaran ta ce iyayen jaririn sun mutu ne sakamakon wani hatsari da ya ritsa da su amma tun kafin mutuwar su, an daskarar da cikin jaririn a cikin na'ura a dakin gwaje-gwaje domin haihuwar sa ta hanyar kimiyya.

An haifi wani jariri bayan mutuwar iyayen sa da shekaru hudu

An haifi wani jariri bayan mutuwar iyayen sa da shekaru hudu

Bayan mutuwar iyayen yaron, kakanninsa daga kowanne bangare sun yi kokarin samun mallakar daskararren ciki domin a yi dashensa a jikin wata matar da zata haife shi.

DUBA WANNAN: Wata sabuwa: Hukumar 'yan sanda ta aikewa Sanatan Shehu Sani sammaci bisa zargin kisa

Daga karshe kakannin yaron sun samo hayar wata mara da aka yiwa dashen kwayoyin halittar daskararren cikin kuma ta haife shi lami lafiya.

Bayan haihuwar sa, kakannin sun gudanar da gwajin kwayoyin halitta na DNA kuma sun tabbatar da jaririn jininsu ne.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel