Nigerian news All categories All tags
Waka a bakin mai ita: Yadda na samu fiye da miliyan N100m daga garkuwa da mutane - Muritala Umar

Waka a bakin mai ita: Yadda na samu fiye da miliyan N100m daga garkuwa da mutane - Muritala Umar

A jiya ne hukumar 'yan sanda a jihar Edo ta gabatar da wani Bafulatani, Muritala Umar, da ya bayyana cewar ya samu fiye da miliyan N100m daga garkuwa da mutane.

Umaru, makiyayi, an kama shi da wata bindiga samfurin AK-47 mai lamba KO340119 da kuma zagaye goma na alburusai.

Ya tabbatar wa da hukuma cewar ya fara garkuwa da mutane da mutane shekaru goma da suka wuce a garin Okene dake jihar Kogi tare da shaida cewar yana da hannu a satar mutane a jihar Edo.

Waka a bakin mai ita: Yadda na samu fiye da miliyan N100m daga garkuwa da mutane - Muritala Umar

Wani mai garkuwa da Mutane

Muritala ya ce yana da shanu masu yawa sannan kungiyar su ta masu garkuwa da mutane ta mallaki bindigu samfurin AK-47 guda goma.

Ya kara da cewar wani babban mutum ne ke basu bayanan sirri a kan wanda ya kamata su sace.

DUBA WANNAN: Dalibin jami'ar ATBU Bauchi ya mutu a ruwan wanka dake Yankari

Ya kara da cewar sun taba karbar miliyan N10m da suka yi garkuwa da wani mutum sannan ya bayyana cewar shugabansu kan kashe duk wanda bai basu hadin kai ba.

Kwamishinan 'yan sanda a jihar, Babatunde Kokumo, ya ce Muritala na fakewa a matsayin makiyayi domin aikata muguwar sana'ar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel