Dalibin jami'ar ATBU Bauchi ya mutu a ruwan wanka dake Yankari

Dalibin jami'ar ATBU Bauchi ya mutu a ruwan wanka dake Yankari

- Wani dalibin aji 400 a jami'ar ATBU dake Bauchi ya rasa ransa yayin wanka a wani ruwa dake wurin shakatawa a Yankari

- Rahotanni sun bayyana cewar dalibin, Gabriel Emmanuel, na aji hudu (400) ne a sashen karatun injiniya

- Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Bauchi, DSP Kamal Abubakar, ya tabbatar da mutuwar dalibin

Wani dalibin aji 400 a jami'ar ATBU dake Bauchi ya rasa ransa yayin wanka a wani ruwa dake wurin shakatawa a Yankari dake jihar Bauchi.

Rahotanni sun bayyana cewar dalibin, Gabriel Emmanuel, na aji hudu (400) a sashen karatun injiniya dake jami'ar ya mutu ne sakamakon nutsewa da ya yi a cikin ruwan.

Dalibin jami'ar ATBU Bauchi ya mutu a ruwan wanka dake Yankari
Dalibin jami'ar ATBU Bauchi ya mutu a ruwan wanka dake Yankari

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Bauchi, DSP Kamal Abubakar, ya tabbatar da mutuwar dalibin tare da bayyana cewar hukumar 'yan sandan ta samu kira ne daga wani da bai ambaci ko shi waye ba.

DUBA WANNAN: Hukumar sojin Najeriya zata bude sashen sojoji mata zalla

Abubakar ya ce jami'an 'yan sanda basu bata lokaci ba wajen zuwa wurin tare da kubutar da dalibin kafin daga bisani ya mutu a asibitin Remee inda ake kokarin ceto ransa.

Ya kara da cewar an dauke gawar dalibin daga asibitin Renee zuwa dakin ajiye gawa na asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng