Hukumar sojin Najeriya zata bude sashen sojoji mata zalla

Hukumar sojin Najeriya zata bude sashen sojoji mata zalla

Hukumar sojin Najeriya ta ce ta kammala shirin bude sashen mata zalla domin inganta aiyukanta a ciki da kuma wajen kasar nan.

Shugaban rundunar sojin ta kasa, Laftanal janar Tukur Yusuf Buratai, ya sanar da haka a yau yayin wani taro a Abuja.

Buratai ya bayyana cewar bude sashen tamkar yabawa ne ga gudunmawar da mata sojoji ke bayarwa aikin soja da kuma yin koyi da sauran kasashen duniya.

Hukumar sojin Najeriya zata bude sashen sojoji mata zalla
Sojoji mata zalla

"Kaddamar da shirin zai bamu damar cin moriyar gudunmawar da mata zasu iya bayarwa ga hukumar soji da kuma tsaron kasa," in ji Buratai.

Buratai ya kara da cewar hukumar soji zata cigaba da gudanar da aiyukan ta ba tare da nuna kowanne irin nau'in banbanci ko wariya ba.

DUBA WANNAN: Sunan da na fi son ake kiran mahaifina da shi - Diyar shugaba Buhari, Zarah Indimi

A wani labarin mai alaka da wannan kun ji cewar, shugaban sojin kasar na, Lt.-Gen. Tukur Buratai, ya haramtawa duk wani sojan kasar nan zuwa majami'a dake wajan barikin soja don aiwatar da ibada.

Janaral Buratai ya bayar da wannan gargadin wajan wani taron soji da ya wakana jiya a Abuja. Buratai yace, duk wani jami'in soja da yake son shiga wani sha'anin, imma na siyasa, na addini ko kabilanci ne, yana mai bashi shawara da yayi ritaya ta kashin-kansa, in yaki kuwa, duk abinda ya same shi ya zargi kansa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng