Nigerian news All categories All tags
Dubu ta cika: Yadda muke yiwa mutane fashi da bindigar roba

Dubu ta cika: Yadda muke yiwa mutane fashi da bindigar roba

- Dubun wani barawo ta cika bayan da yan sanda su kayi ram da shi

- Da rana yayi kwandasta da daddare kuma ya yiwa mutane kwace

Wani yaro mai shekaru 20, ya bayyana yadda shi da tawagarsa suke yi wa mutane fashi da bindigar roba. Da yake jawabi bayan da dakarun bayar da agajin gaggawa na rundunar yan sanda ta Jihar Lagos suka kama shi ranar Alhamis da ta gabata, Inda yake cewa, shi da yan tawagar tasa suna yiwa masu babura barazana ne da bindigar roba a yankin Adeniji Adele dake karkashin babbar gada ta uku (Third Mainland Bridge).

Dubu ta cika: Yadda muke yiwa mutane fashi da bindigar roba

Rilwan Wasiu, wanda ake zargi da fashi da bindigar roba

Wanda ake zargin, mai suna Rilwan Wasiu dan jihar Oyo, an damke shi ne a ranar Alhamis karfe goma na dare bayan da yan sanda suka hango shi daga nesa yana ta jibgar budurwarsa, sai su kayi kokarin shiga tsakaninsu domin sasanta su, kwatsam sai ga bindigar roba ta fado daga jikin wanda ake zargin.

Fadowar bindigar ne ya sanya Wasiu yunkurin arecwa da gudu amma da yake dubunsa ta cika, nan take dakarun bayar da agajin gaggawa na hukumar yan sanda a jihar ta Legos su kayi ram da shi tare da tafiya da shi can ofishin rundunar.

Sai dai Wasiu ya ce, ya tsinci bindigar robar ne a karkashin gadar domin can ne makwancinsa “Da na tsinci bindigar ne sai nayi yunkurin zuwa na wurgar da ita kafin daga bisani yan sanda su kama ni muna fada da budurwa ta.” A cewar wanda ake zargin.

Amma bayanda yan sandan suka tsananta bincike ne, suka gano yana daga cikin gungun mutane uku da suke yiwa jama'a da masu babura kwace a gefen hanyar Adeniji Adele dake babar kusa da karkashin babbar gada ta ukun (Third Mainland Bridge).

KU KARANTA: Dolene a sanar da jama'a masu sace musu dukiyar kasa - Adam Oshiomhole

Yanzu haka dai yan sanda sun gano cewa su uku ne, ragowar biyun su ne, Salami da Sakiru, bayan sun kammala cin kasuwar dare, da rana kuma sai su koma bin motar Bus a matsayin karen mota.

Da yake magana akan batun, kakakin rundunar yan sanda ta jihar Lagos, SP Chike Oti, ya ce, wannan nasara ta biyo bayan umarnin da kwamishinan yan sanda na jihar ya bayar ne da a kara jami’an sintiri domin bincikar aiyukan masu laifi a karkashin gadar.

Dubu ta cika: Yadda muke yiwa mutane fashi da bindigar roba

Dubu ta cika: Yadda muke yiwa mutane fashi da bindigar roba

Yanzu haka dai wanda ake zargin, an mika shi zuwa sashin binciken masu manyan laifuka na (FSARS), kana kuma yan sanda zasu cigaba da bibiyar ragowar biyu abokan aikata laifin na Rilwan Wasiu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel