Nigerian news All categories All tags
Hukumar kwastam tayi babban kamu a jihohin Kano da Jigawa, ta cafke mutane hudu

Hukumar kwastam tayi babban kamu a jihohin Kano da Jigawa, ta cafke mutane hudu

Jami'an hukumar Kwastam sun ce sun kama buhunhunan shinkafar kasashen ketare fiye da 500 da kuma dila 20 ta kayan gwanjo da darajar su ta kai kimanin miliyan N10m.

Shugaban hukumar kwastam reshen jihohin Kano da Jigawa, Yusuf Abba Kassim, ya ce sun kama mutane hudu yayin aikin sintirin hukumar, kuma yanzu haka suna tsare da su a sashen shari'a na hukumar domin gurfanar da su gaban kotu.

Hukumar kwastam tayi babban kamu a jihohin Kano da Jigawa, ta cafke mutane hudu

Hukumar kwastam tayi babban kamu a jihohin Kano da Jigawa, ta cafke mutane hudu

Kassim ya ce, jami'an hukumar sun kama wasu daga cikin kayayyakin ne a wani gari, Kantakara, dake iyakar Najeriya da Nijar, a karamar hukumar Maigatari dake jihar Jigawa. Ya kara da cewa, an kama kayan gwanjon da buhunhunan shinkafar waje a boye cikin buhunhunan wake a wajen garin Kano.

DUBA WANNAN: Abinda nake son Buhari ya yiwa masu cin hanci a Najeriya - Oshiomhole

Da yake ganawa da manema labarai ranar Juma'a a garin Kano, Kassim, ya ce, jajircewar jami'an hukumar ne ta basu nasarar kama kayan.

Kazalika ya bayyana cewar ofishin hukumar ya sami kudin shiga da adadinsu ya kai biliyan N4.3bn tare da samun rarar miliyan N609m a a kan abinda ake bukatar su samar a watanni hudu na farkon shekarar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel