Nigerian news All categories All tags
Hotuna daga gangamin taron jam'iyyar PDP a jihar Katsina

Hotuna daga gangamin taron jam'iyyar PDP a jihar Katsina

A jiya ne, Asabar, jam'iyyar PDP ta gudanar da taron gangami na jihohin Arewa maso yamma a jihar Katsina, mahaifar shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Taron gangamin jam'iyyar na PDP ya samu halartar dubban dubatan magoya baya daga jihohin Arewa, mjusamman jihohin Arewa maso yamma da suka hada da jihohin Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto, da Zamfara.

Hotuna daga gangamin taron jam'iyyar PDP a jihar Katsina

Taron gangamin jam'iyyar PDP a jihar Katsina

Manyan 'ya'yan jam'iyyar da suka hada da shugabanninta da zababbun gwamnoni da 'yan majalisu daga jihohi sun halarci taron.

Manyan 'yan jam'iyyar da suka halarci taron sun hada da masu neman jam'iyyar ta tsayar takarar shugaban kasa; Sule Lamido, Ibrahim Shekarau, da gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo.

Hotuna daga gangamin taron jam'iyyar PDP a jihar Katsina

Taron gangamin jam'iyyar PDP a jihar Katsina

'yan Najeriya na cigaba da tofa albarkacin bakinsu a kan taron gangamin na PDP musamman ganin irin yadda dumbin jama'a suka halarci taron. Wasu na ganin cewar, dandazon mutanen da suka halarci taron alama ce ta nuna cewar jama'a na tare da jam'iyyar, wani abu da ya kamata ya saka cikin jam'iyyar APC ya duri ruwa.

Hotuna daga gangamin taron jam'iyyar PDP a jihar Katsina

Taron gangamin jam'iyyar PDP a jihar Katsina

Saidai wasu na ganin cewar taron jama'ar ba wani abun damuwa bane musamman ganin yadda kowacce jam'iyya ke tara mutane duk lokacin da zata yi taron gangami.

DUBA WANNAN: Ridda: Matashi ya bar addinin Musulunci, ya koma Kirista

Jama'a kan halarci taron gangamin jam'iyyu muddin za a basu dan wani abu su saka a aljihunsu bayan taron.

Hotuna daga gangamin taron jam'iyyar PDP a jihar Katsina

Taron gangamin jam'iyyar PDP a jihar Katsina

A jiyan da jam'iyyar PDP ke gudanar da taron gangamin, shugaban kasa Buhari na jihar domin yin ta'aziyya ga iyalin Sanatan jihar, Mustapha Bukar, da Allah ya yi masa rasuwa.

Hotuna daga gangamin taron jam'iyyar PDP a jihar Katsina

Taron gangamin jam'iyyar PDP a jihar Katsina

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel