Ganduje, El-Rufai da sauran Gwamnonin da su ka fi kowa tatsar kudin shiga a Arewa
Wannan karo kuma mun kawo maku jerin Jihohin Arewacin Najeriya da su ka fi kowane samun kudin daga haraji a shekarar da ta wuce. Dama kun ji cewa Kano ce kadai Jihar Arewa da ke cikin manyan masu kudin shiga a kaf kasar a bara.
Jihohin Arewacin kasar nan da su ka fi kowa samun kudin shiga a shekarar da ta wuce kamar yadda BudgIT su ka bayyana su ne Kano da Kaduna. Ga dai cikakken jerin nan kamar haka:
1. Gwamna Abdullahi Ganduje
Jihar Kano wanda ita ce cibiyar kasuwancin Yankin ce gaba a jerin. Gwamatin Jihar Kano ta samu sama da Naira Biliyan 42 a shekarar da ta wuce.
KU KARANTA: Jihohi 5 da su ka fi kowa samun kudin shiga 2017 a Najeriya
2. Gwamna Basir El-Rufai
A shekarar da ta wuce Gwamna Nasir El-Rufai ya kafa tarihi a Kaduna inda ya samu sama da Biliyan 26 daga hannun jama’a a Jihar Kaduna.
3. Gwamna Abdulfatah Ahmad
Ta uku a wannan jerin ita ce Jihar Kwara inda Gwamna Abdulfatahi Ahmed ya samu kusan Naira Biliyan 20 daga haraji a shekarar bara.
4. Gwamna Samuel Ortom
Jihar Benuwe wanda aka sani da harkar noma ta samu abin da ya haura sama da Naira Biliyan 12 na kudin shiga a shekarar 2017 dinnan.
5. Gwamna Simon Lalong
Gwamna Simon Bako Lalong na Jihar Filato ne ya zo na 5 a jerin inda ya tatsi abin da ya haura Biliyan 10 daga mutanen Garin sa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng