Nigerian news All categories All tags
Hanyoyi 5 da azumin sa'o'i 72 ke taimakon garkuwar jikin dan Adam

Hanyoyi 5 da azumin sa'o'i 72 ke taimakon garkuwar jikin dan Adam

Wasu masu binciken kimiyya a sashen karatun halitta a jami'ar kudancin California sun tabbatar da cewar azumin kwanaki uku (sa'o'i 72) yana sabunta garkuwar jikin dan Adam duk tsufansa.

Masu binciken sun bayyana wannan sabon ilimi a matsayin wani gagarumin sirri da zai kara inganta rayuwar mutane.

Sun zayyana ta hanyoyin da azumin kwanaki ukun zai iya taimakawa garkuwar jiki kamar haka;

1. Sabunta halittun cikin jini dake yaki da cututtuka (White blood cells)

2. Azumin kwana ukun na bayar da kariya ga masu cutar daji (Cancer) daga illolin da magungunan cutar kan yiwa jiki.

Hanyoyi 5 da azumin sa'o'i 72 ke taimakon garkuwar jikin dan Adam

Hanyoyi 5 da azumin sa'o'i 72 ke taimakon garkuwar jikin dan Adam

3. Yana taimakawa jiki wajen kirkirar sabbin kwayoyin halitta mafi kankanta a jikin dan Adam (Cells) tare da taimakon jiki wajen fitar da sassan garkuwa da suka tsufa ko suka lalace.

DUBA WANNAN: Zan Iya Fadawa Wuta Saboda Buhari, Zan Iya Yin Komai Akan Buhari - Gwamnan Kogi

4. Wani gwaji da masu binciken suka yi a kan wasu mutane ya tabbatar da samun raguwar wani sinadari a jiki da kan iya haifar da kumburi da ciwon daji.

5. Yana saka jiki amfani da mai da sukari da jiki ke ajiyewa tare da samar da kyakykyawan yanayi ga jikin mutum da zai tsaftace tushen halittar kwayoyin halitta a cikin jiki (stem cells).

Shugaban tawagar masu binciken, Farfesa Longo, ya ce ga duk mai bukatar samun ingantacciyyar lafiya, to ya juri yin azumin kwanaki uku.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel