Farfadiya gare shi, ba mu muka kashe shi ba - Hukumar soji ta musanta kisan farar hula a jihar Taraba

Farfadiya gare shi, ba mu muka kashe shi ba - Hukumar soji ta musanta kisan farar hula a jihar Taraba

A jiya ne hukumar sojin Najeriya ta musanta rahotannin dake yawo a kafar yada labarai cewar, ta azabtar tare da kashe wani farar hula, Yusuf Haruna, a jihar Taraba.

An tura dakarun soji masu yawa jihar Taraba a wani atisaye da hukumar ta sanyawa suna AYEM AKPATUMA domin magance yawaitar afkuwar rigingimu masu alaka da kabilanci a jihar.

A wata sanarwa da darektan hulda da jama'a na rundunar soji, Birgediya Janar Texas Chukwu, ya fitar ya ce basu azabtar da marigayin ba tare da bayyana cewar, hatta 'yan uwansa sun tabbatar da cewar yana fama da cutar farfadiya.

Farfadiya gare shi, ba mu muka kashe shi ba - Hukumar soji ta musanta kisan farar hula a jihar Taraba
Shugaban rundunar sojin kasa; T. Y Buratai

Chukwu ya ce rahotannin da ake yadawa cewar dakarun soji ne suka azabtar da mutumin har saida ya mutu, ba gaskiya bane kuma bata sunan hukumar sojin Najeriya ne.

DUBA WANNAN: Sankarau: Mutane 10 sun mutu, an kwantar da wasu da dama a Baburan jihar Jigawa

Kazalika, Chukwu ya kara da cewar, mutumin gagararre ne dake zaune a Mbara dake Mbanga tare da kara bayyana cewar, yana da hannu a cikin aiyukan ta'addanci da dama dake faruwa a jihar.

Sanarwar ta kara da cewar, dakarun sojin atisayen AYEM AKPATUMA sun taba damke shi amma sai ya tsere kafin a mika shi hannun hukumar 'yan sanda domin amsa tambayoyi kafin daga bisani hukumar sojin ta samu rahoton mutuwar sa a wani asibiti dake Mbanga.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng