Tsaka mai wuya: Jihohin arewa da ake tafka rikicin siyasa tsakanin gwamna da sanata

Tsaka mai wuya: Jihohin arewa da ake tafka rikicin siyasa tsakanin gwamna da sanata

A ranar 25 ga watan Maris, Sanataci uku da ke wakiltar jihar Legas, Gbenga Ashafa, Oluremi Tinubu da Solomon Olamilekan sun taru sun yabi Gwamna Ambode na jihar Legas saboda irin ayyukan alheri da yakeyi a jihar duk da cewa dukkansu ba jam'iyya daya suke ba kuma hakan ya bawa koya sha'awa sai dai ba hakan take ba a wasu jihohin. Hakan yasa Legit.ng ta tattaro muku jihohin da Sanataocin su basu ga maciji da gwamnonin jihar.

1) Jihar Kaduna

Sabanin abin da yake faruwa a Legas, su kuwa Sanatocin Kaduna sun jima suna hayaniya da Gwamnan jihar Mallam Nasir El-Rufai. Cikin kwanakin nan Sanatocin uku; Shehu Sani, Suleiman Hunkuyi da Danjuma Lar suka ki amincewa da bukatar gwamna El-Rufai na karbo bashin dallar Amurka miliyan 350 don gudanar da ayyuka.

Ga wadanda suke bibiyan siyasar jihar Kaduna suna iya ganin cewa rashin amincewa da bashin ba zai rasa nasaba da irin rigingimun da suka rika faruwa tsakanin su idan akayi la'akar da yadda El-Rufai ya hana Sanatocin sakat duk da cewa dalilin da suka bayar shine bashi yayi wa jihar yawa kuma wai jihar bata bi ka'idojin da suka dace ba wajen karbar bashin.

2) Jihar Kogi

A jihar Kogi kuma Gwamna Yahaya Bello ne ke gwabzawa da Sanata Dino Melaye. Tun farko dai Senata Dino Melaye yace rashin biyan albashin mai’aikata da fansho ne dalilin da yasa suke samun sa-in-sa da gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello.

Dino ya ci gaba da cewa, gwagwarmayar sa yana yi domin kare mai’aikatan Jihar kogi da yan fansho wanda ke cikin matsanancin hali a dalilin rashin biyan albashi da fansho har na wata 15 da gwamnan yayi.

Hakan yasa Melaye da sauran mazabai guda uku suka hada kungiya don ceto al'ummar har sukayi nasarar samar da buhunan shinkafa 1260 da taimakon sauran yan majalisa amma bayan an kawo shinkafar jihar ta Kogi sai akace yan daba sun sace.

Rashin jituwar nasu tayi kamari har ta kai ga Dino Melaye ya shigar da kara ofishin yan sanda inda yayi ikirarin cewa Gwamna Bello ne ya aike da yan Sandan SARS don su kashe shi duk da cewa bai fada dalilin hakan ba.

Tsaka mai wuya: Jihohin arewa da ake tafka rikicin siyasa tsakanin gwamna da sanata

Gwamnonin arewa

Daga baya kuma hukumar yan sandan ta bayar da sanarwan cewa zata gurfanar da Dino Melaye gaban kotu bisa zargin sa da daukan nauyin yan ta'adda da aka kama da makamai.

3) Jihar Kano

Rikici tsakanin Gwamna Abdullahi Ganduje da Sanata Rabiu Kwankwaso ya fito filli ne bayan Ganduje ya nada mukammai a jihar amma duk yayi watsi da kwamishinonin Kwankwaso sai daya kawai ya bari, Nasiru Gawuna wanda shine kwamishinan noma a gwamnatin Kwankwaso.

Rashin jituwar da ke tsakaninsu ne yasa Kwankwaso bai je jihar Kano ba tun Mayun 2015 kuma daga baya a watan Janairun 2018 da yayi niyyar zuwa sai wata sabuwar rigimar da saka barkewa tsakanin mabiyya Kwankwasiyya da Gandujiyya saboda an kafa taron yakin neman zabe da akayi a rana guda. Rikicin yayi sanadiyar rasa raunata al'umma da dama kuma hakan yasa Kwankwaso ya janye ziyarar nasa don samar da zaman lafiya.

DUBA WANNAN: Almundahana da kudin kasa a mulkin PDP: Gwamnatin tarayya ta umarci EFCC​ ta gurfanar da mutanen da aka saki sunayensu

4) Jihar Zamfara

Rashin jituwa tsakanin Gwamna Abdulaziz Yari da Sanata Kabiru Marafa ta samo asali ne kan batun nada Ahmad Bello Mahmud a matsayin kwamishina zabe wanda gwamna Abdulaziz bai amince ba har ya kai ga rubuta wasika zuwa fadar shugaban kasa inda ya ce Mahmud bako ne ba dan jihar Zamfara ba.

Hakan baiyi wa Sanata Kabiru Marafa dadi ba har shima daga baya ya shigar da korafi gaban Majalisar dattawa inda ya bayyana cewa gwamna Yari shima bako ne don asalin iyayensa ba yan Zamfara bane, shima an haife shi ne kamar yadda ake haifi Mahmud.

A ranar 31 ga watan Janairun 2018, yayinda yake bayar da gudunmawar sa kan kashe-kashen da akeyi a jihar Zamfara, Mahmood yayi ikirarin cewa Gwamna Yari da mataimakinsa suna daukan nauyin yan daba a jihar. Hakan yasa mai magana da yawun gwamnan, Alhaji Salisu Isah ya mayar masa da martani inda yace tabbas gwamna Yari zai tabbatar da cewa yaga bayansa a siyasance.

5) Jihar bauchi

A jihar Bauchi ma babu alaka mai kyau tsakanin Gwamna Mohammed Abubakar da kakakin Majalisar Dattawa, Yakubu Dogara. A ranar 20 ga watan Augusta, kakakin majalisar ya jagoranci sauran Sanatocin jihar Bauch zuwa sakatariyar APC na Abuja inda ya zargi gwamnan da karkatar da kudin tallafi da shugaba Buhari ya rabawa gwamnoni.

Rashin jituwa tsakanin Gwamna Mohammed Abubakar da Yakubu Dogara ta samo asalin ne lokacin da aka zabi Dogara a matsayin kakakin majalisa wanda ya sabawa tsarin karba-karba na jami;iyyar APC, Dogara ya fusata ne yayinda ya fahimci cewa gwamnan da yake niyyar ya daga yaki bashi goyon bayan don zama kakakin Majalisa.

A wata hira da akayi da Dogara a wata jarida a Mayun 2017, ya amsa cewa akwai rashin jituwa tsakanin sa da gwamna Abubakar amma hakan ya faru ne saboda rashin biyan bukatun al'umma ba wai don yaki bani goyon baya wajen zama kakakin majalisa ba

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel