Tazarcen Ganduje: Dalilai hudu da kan iya kai shi ga Nasara

Tazarcen Ganduje: Dalilai hudu da kan iya kai shi ga Nasara

Batun dambaruwar siyasa tsakanin tsohon gwamna jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso, da kuma gwamna mai ci, Abdullahi Umar Ganduje, ba boyayye ko sabon abu bane.

Wasu da dama na ganin cewar kujerar gwamna Ganduje na fuskantar barazana a zaben shekarar 2019 saboda sabanin da ya shiga tsakaninsa da Kwankwaso.

A yayin da jama'a ke cigaba da tofa albarkacin bakinsu a kan al'amuran siyasar ta Kano, Legit.ng ta kawo maku wasu dalilai guda hudu da kan iya bawa Ganduje damar sake cin zabe cikin sauki.

Tazarcen Ganduje: Dalilai hudu da kan iya kai shi ga Nasara
Tazarcen Ganduje: Dalilai hudu da kan iya kai shi ga Nasara

1. Aiyukan raya kasa: Ko shakka babu, gwamna Ganduje na shimfida aiyuka masu matukar muhimmanci a birane da kauyukan jihar Kano. Bayan nasa aiyukan da ya kirkira, Ganduje ya karasa aiyukan da gwamnatin tsohon gwamna Ibrahim Shekarau ya fara, wani abu da Kwankwaso bai yi ba lokacin yana mulki. Kazalika, Ganduje ya cigaba da aiyukan da Kwankwaso ya fara.

2. Janyo gogaggun 'yan siyasa a jika, goyon bayan 'yan majalisar jiha da shugabannin kananan hukumomi: Ganduje, za a iya cewa ya daure akuyar sa a gindin magarya ta hanyar kakkabe 'yan Kwankwasiyya tare da dora nasa mutanen a matsayin shugabannin kananan hukumomin jihar Kano 44.

Kazalika, Ganduje yana da goyon bayan majalisar jihar, domin yanzu haka 'yan majalisar jihar dake yin Kwankwasiyya basu wuce mutane biyar ba.

Masana lissafin siyasa sun jinjinawa wannan hikima ta kame masu rike da mukaman siyasa a jihar a hannu, domin yin hakan zai saukaka masa yakin neman zabe da kuma cin zabe.

A wani mataki da gwaman ya kara samun jinjina shine janyo wasu 'yan siyasa, irinsu Kankarofi da Usman Alhaji, daga gwamnatocin baya zuwa bangarensa.

Dadin dadawa, ragowar Sanatocin Kano biyu; Kabiru Gaya da Barau Jibrin na tare da Ganduje.

DUBA WANNAN: An gano adadin kudin da 'yan siyasar Najeriya suka lalata daga 2003 zuwa yanzu

3. Kyakykyawar alaka da malaman addini da sarakunan gargajiya: Duk wanda ya san siyasar Kano ya san cewar addini da masarauta na taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar lashe zabe.

A bangaren addini, har lakabi ake yiwa gwamna Ganduje da "Khadimul Islam" saboda dangantaka me kyau dake tsakaninsa da malaman addini a jihar Kano.

Daurin auren diyar Ganduje da aka yi a fadar mai martaba, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, wata alama ce dake nuna kyakykyawar fahimta juna tsakanin bangaren gwaman da sarkin Kano.

4. Kyautatawa ma'aikata: Tun bayan hawansa mulkin Kano, gwamna Ganduje, bai taba jinkiri ko gaza biyan ma'aikatan jihar Kano albashinsu ba.

Gwamnatin ta Ganduje ta dauki karin ma'aikata a bangarori da dama a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164