An gano adadin kudin da 'yan siyasar Najeriya suka lalata daga 2003 zuwa yanzu

An gano adadin kudin da 'yan siyasar Najeriya suka lalata daga 2003 zuwa yanzu

- Wata kungiya tace gwamnatin tarayya, jihohi 36 da babban birnin tarayya, Abuja basu da wani abin kwarai da zasu nuna wa al'umma idan akayi la'akari da kudaden da suka hadiye a cikin shekaru 16 da suka shude

- Kungiyar tayi ikirarin cewa adadin kudin da 'yan siyasar Najeriya suka salwantar ya tun daga 2003 zuwa yanzu ya ka triliyan N66.7

- Kungiyar tayi kira ga yan Najeriya suyi watsi da hayaniyar da jam'iyyar PDP da APC sukeyi

Wata kungiya mai rajin kare hakkin al'umma da tabbatar da biyaya ga doka, International Society for Civil Liberties and Rule of Law tayi ikirarin cewa jihohi 36 da babban birnin tarayya, Abuja da kananan hukumomin ta 774 na Najeriya basu da wani abin kwarai da zasu nuna wa al'umma idan akayi la'akari da triliyan N140.8 ko $724bn da suka rika warewa a matsayin kasafin kudi a shekaru 16 da suka wuce.

'Yan siyasa sun bannatar da N66.7tn tun daga 2003 - Kungiya
'Yan siyasa sun bannatar da N66.7tn tun daga 2003 - Kungiya

Kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito, kungiyar ta fitar da wani sanarwa inda tayi ikirarin cewa tsabar kudin da yan siyasar Najeriya suka rika karkatar daga cikin kasafin kudi tun daga 2003 ya tasanma $302bn ko kuma naira triliyan 66.7.

KU KARANTA: Najeriya ta gargadi majalisar dinkin duniya kan hatsarin da ke tattare da malakar makamen kare dangi

Jagoran masu bayar da shawara na kungiyar, Mr. Emeka Umeagbalasi ne ya bayyana hakan a yayin da yake tsokaci a kan jerin sunayen barayin kudin gwamnati da jam'iyoyin APC da PDP suka fitar.

"Ana amfani da kudirin dokar tattance kudi wajen karkatar da kudaden al'umma ta hanyar yin aringizo a wajen biyan kudaden ayyuka, alawus da suka maimaita alawus din.

"Misali shine tsabar kudi har naira miliyan 13 da naira miliyan 12 da yan majalisa suka ware wa kansu a matsayin kudin gudanar da ayyuka duk da cewa dokar manyan ma'aikatan gwamnati na 2008 ya kayade kudin a N1m duk wata." inji shi.

Kungiyar tayi kira da yan Najeriya da su bude idanun su kada su bari hayaniyyar da jam'iyoyin APC da PDP keyi ta dauke musu hankali akan abin da yake da muhimmanci. A cewar kungiyar, jam'iyyun guda biyu duk suna da hannu wajen sace kadaden yan najeriya kuma dole ne a tasa su gaba don suyi bayani.

Daga karshe kungiyar tace dole ne su fada wa Najeriya abin da yasa har yanzu Najeriya ke baya wajen cigaba idan akayi la'akari da kasashen duniya da suka sami yancin su lokaci daya da Najeriya misali kasashen Malaysia, Taiwan, Korea ta Kudu, Indonesia, Singapore, Bahrain, Qatar, Oman, Brunei, Saudiyya, Dubai da sauran su

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel