Daukar fansa: Sojojin Najeriya sun yi masu yan bindiga luguden wuta a Kaduna

Daukar fansa: Sojojin Najeriya sun yi masu yan bindiga luguden wuta a Kaduna

A ranar Talata 3 ga watan Afrilu ne rundunar mayakan sojan kasa ta Najeriya suka hallaka wasu gaggan yan bindiga guda biyu a jihar Kaduna, a wani aiki da suke gudanarwa na kakkabe yan bindiga daga jihar.

Daily Nigerian ta ruwaito Daraktan watsa labar na rundunar Sojan kasa, Texas Chukwu ne ya bayyana haka cikin wata sanawar da ya fitar, inda yace Sojoji sun bindige yan bindigan ne a yayin da suke sintiri a kauyen Dogon Dawa, hanyar Damari.

KU KARANTA: An bankado yadda Sambo Dasuki ya taimaka ma Buhari wajen darewa kujerar shugaban kasa a karo na farko

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sojojin sun kwato makamai da suka hada da bindigu kirar AK 47 guda biyu da alburusai da dama. A wani rahoton, inji Kaakakin Sojin, Sojoji sun yi musayar wuta da wasu yan bindiga da suka yi kwantan bauna a sabuwart hanyar filin jirgin sama dake Rigasa Kaduna.

“A yayin wannan hanyar, Sojoji guda biyu sun samu raunuka, haka zalika Sojoji sun yi arangama da yan bindiga a kauyn Buruku na jihar Benue, sai dai Sojoji sun samu nasarar fatattakar yan bindigan” Inji Texas.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng