Buhari ba zaiyi cacar-baki da Obasanjo ba saboda yana gaba dashi a aikin Soja - Femi Adesina
- Fadar shugaban kasa tayi tsokaci a kan cacakar da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya keyiwa Buhari
- Adesina ya ce Buhari ba zaiyi cacar-baki da Obasanjo ba kasancewar sa yana gaba dashi a cikin aikin Soja
- Adesina ya kuma ce duk abinda Obasanjo ya fadi ra'ayin sa kuma yana da damar fadin ra'ayin nasa
A ranar Litinin fadar shugaban kasa tayi tsokaci kan cacakar da tsohon shugaban kasa Obasanjo yake yiwa gwamnatin shugaba Buhari. A cewar mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, shugaba Buhari ba zai kulla gaba da Obasanjo ba.
A ranar Litinin da ta gabata, Obasanjo ya sake cacakar gwamnatin Buhari yayin da yake karban bakuncin kungiyar sabuwar Najeriya a dakin karatu na Obasanjo a garin Abeokuta na jihar Ogun.
KU KARANTA: Gwamna Shettima yayi tir da harin da aka kaiwa kauyukan Borno
Obasanjo ya ce shugaba Buhari bai fahimci yadda ake gudanar da siyasar cikin gida ba kuma ya kara da gargadin yan Najeriya da kar su sake su zaben Buhari a 2019 don zasu kara dilmiya Najeriya cikin matsala ne.
A yayin da yake mayar da martani, Adesina yace kalaman Obasanjo basu da banbanci da abin da ya rubuta a wasikar da ya aike wa shugaba Buhari a watan Janairu wanda tuni Ministan Labarai da Al'adu Lai Mohammed ya bashi amsa.
"Amsar da Lai Mohammed ya bashi a baya ta wadatar kuma duk abin da Obasanjo ya fadi ra'ayinsa ne kuma yana da damar fadin ra'ayin nasa," inji Adeshina.
Adesina kara da cewa Obasanjo na gaba da Buhari a cikin aikin Soja saboda haka babu yadda za'ayi yayi rigima da shi kamar yadda ya bayyana a hirar tarho da yayi da gidan talabijin na Channels.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng