Nigerian news All categories All tags
Abin na yi ne: Wani fitaccen Malamin Izala ya ɗaura ɗamarar ƙwato wata muhimmiyar mukamin siyasa a Kano

Abin na yi ne: Wani fitaccen Malamin Izala ya ɗaura ɗamarar ƙwato wata muhimmiyar mukamin siyasa a Kano

A yayin da zabukan shekarar 2019 ke karatowa, yan takarkaru da dama sun fara bayyana muradin darewa mukaman siyasa daban daban, tare da nuna maitarsu a fili, su ma Malamai ba’a barsu a baya ba.

A nan ma fitaccen Malamin nan, wanda ya shahara a fagen haddar Al-Qur’ani mai tsarki, Sheikh Ahmad Sulaiman Ibrahim ne ya buga nasa tambarin siyasar, inda ya fantsama cikin farfajiyar siyasar jihar Kano.

KU KARANTA: Yan bindiga sun bindige mutane 2, sun yi garkuwa da wasu mutane 9 a Kaduna

Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani na Facebook, Aminu Umda Al’Azhari ne ya tabbatar da haka a shafinsa, inda yace Shehin Malamin da kansa ne ya tabbatar masa da muradinsa na tsayawa takara a 2019.

Abin na yi ne: Wani fitaccen Malamin Izala ya ɗaura ɗamarar ƙwato wata muhimmiyar mukamin siyasa a Kano

Fastan Malam

Majiyar Legit.ng ta bada tabbacin Malam Ahmad Sulaiman zai yi takarar mukamin kujerar dan majalisar dokokin jihar Kano ne mai wakiltar karamar hukumar Tarauni, a karkashin inuwar jam’iyyar APC ta baba Buhari da Ganduje.

Daga karshe majiyar mu ya yaba da kokarin Malam, sa’annan ya yi addu’ar Allah ya tabbatar masa da burinsa idan da alheri a cikinta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel