Gwamna Masari ya samu lambar girma ta fannin kimiyya da fasaha daga kasar Tunisia

Gwamna Masari ya samu lambar girma ta fannin kimiyya da fasaha daga kasar Tunisia

- Kungiyar kimiyya da fasaha na Tunisia sun bawa gwamnan jihar Katsina lambar girma ta fannin kimiyya da fasaha

- Kungiyar tace ta bashi lambar girman ne sakamakon tallafin da yake bayarwa don cigaban kimiyya da fasaha

- Ya karbi lambar girman ne a garin Monastir dake kasar Tunisia inda gabatar makarantar gwamnati ta garin Funtua ta wakilci Najeriya a gasar kimiyya

Gwamna Masari ya samu lambar yabo na kimiyya da fasaha daga kasar Tunisia
Gwamna Masari ya samu lambar yabo na kimiyya da fasaha daga kasar Tunisia

Kungiyar kimiyya da fasaha na kasar Tunisia sun bawa gwamnan jihar Katsina lambar girma ta fannin kimiyya da fasaha, sakamakon tallafin da yake bayarwa don cigaban kimiyya da fasaha a Jihar.

Ya karbi lambar girman ne a birnin Monastir dake kasar Tunisia, wanda Musa Abdu, Daraktan ma’aikatar Ilimi ya karba a madadin Kwamishinan Ilimi, Farfesa Badamasi Lawal Charanci.

KU KARANTA: Zaben 2019: Kuyi takatsantsan da gwamnatin Buhari - Sakon kungiyar Obasanjo ga 'yan Najeriya

An bayar da lambar girman ne a wurin bukin kasashen duniya da aka gabatar a kasar ta Tunisia, na kimiyya da fasaha, wanda makarantar gwamnati ta garin Funtua ta wakilci Najeriya.

Wakilan daga jihar Katsina sun samu kyaututuka tagulla guda uku, bayan gabatar da aikin bincike da suka gudanar a kan naura mai aikin da hasken rana (Solar Collector System), a wurin taron. Kafin nan jihar katsina ta zama zakara a makamancin gasar da aka gudanar a birnin tarayya, watan da ya gabata

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164