Ba za a taba raba Turai da addinin Musulunci ba Inji Kungiyar EU

Ba za a taba raba Turai da addinin Musulunci ba Inji Kungiyar EU

- Kungiyar EU tace Musulunci ginshiki ne a tarihin Kasashen Turai

- Har kuma gobe dai ba za a daina maganar musulunci ba a Yankin

- An yi wani zama tsakanin Shugabannin EU da Limamai na Turai

Mataimakin Shugaban Kungiyar kasashen Turai na Duniya watau EU Mista Frans Timmermans ya zauna da manyan Limaman addinin Musulmi na kasashen Turai irin su Faransa, Beljika, Bulagariya, da Jamus da kuma Kasar Italiya.

Ba za a taba raba Turai da addinin Musulunci ba Inji Kungiyar EU
Daya daga cikin Shugabannin Kungiyar EU ya zauna da Limamai

Kungiyar ta kasashen Turai ta gana da Malaman addinin Musuluncin domin ganin matsayar Kasar Turai nan gaba. Frans Timmermans ya bayyana cewa addinin Musulunci da shi a kan sa Turai kuma har nan gaba Musulunci na nan.

KU KARANTA: An damfari Shugaban kasar Najeriya Buhari da lambar yabon karya

EU tace za tayi kokarin ganin ta cigaba da yada addinin na Musulunci a Turai. Wannan taro dai shi ne karo na farko da wannan kungiya tayi da Limaman Musulunci a tarihi kuma za a cigaba da yin irin wannan zama domin cigaban Yankin.

Kungiyar EU na neman ganin yadda za a horar da Malamai sannan kuma a kawar da masu tsattsauran ra’ayin Islama a kuma yi maganin sauran matsalolin da ke damun Musulmai. Hukumar dillacin labarai na kasar Kuwait ta rahoto wannan labari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel