Alakar Shugaba Buhari da Bola Tinubu tana kara karfi gabanin zaben 2019

Alakar Shugaba Buhari da Bola Tinubu tana kara karfi gabanin zaben 2019

Ga dai zabe ya karaso kuma daga yadda mu ke fahimtar abubuwa Shugaba Buhari ya gyaro ta da kyau da babban ‘Dan siyasar kasar Yarbawa Bola Tinubu tun daga rikicin Jam’iyya har zuwa maganar zaben sababbin Shugabanni a APC

Za ku ji yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara kulla sabon abokantaka ko kuma ace ya karfafa alakar da a da ta fara rage karfi da babban Jigo a Jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a cikin ‘yan kwanakin nan.

Alakar Shugaba Buhari da Bola Tinubu tana kara karfi gabanin zaben 2019

Buhari yana tare da su Tinubu kan maganar wa’adin su John Oyegun

Kusan tun bayan hawa mulkim bangaren Tinubu ya fara samun kan shi a wajen Gwamnatin Buhari duk da irin kokarin da Tinubu yayi na ganin Muhammadu Buhari ya samu tikitin Jam’iyya da kuma lashe zaben 2015 bayan an kafa APC.

KU KARANTA: An yi kira ga Shugaba Buhari ya sake tsayawa takara a 2019

Daily Trust ta tuna mana yadda Shugaban kasa Buhari ya hau jirgi da Bola Tinubu zuwa Kasar Ivory Coast a bara. Bayan nan kuma Shugaban kasar ya nada Bola Tinubu ya dinke barakar da ke cikin Jam’iyyar APC ganin zabe ya karaso.

A jiya ne Shugaban kasar kuma ya halarci bikin cikar tsohon Gwamnan na Legas shekaru 66 a Duniya. Kafin nan a wannan makon Buhari ya goyi bayan Tinubu inda ya nemi a dakatar da maganar karawa Shugabannin APC wa’adi ayi zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel