Dawo da darasin tarihi a makaranta zai taimakawa yara – Shehu Sani

Dawo da darasin tarihi a makaranta zai taimakawa yara – Shehu Sani

- Sanata Shehu ya yabawa wani kokari na Gwamnatin nan a fannin ilmi

- Gwamnatin Buhari ta maido darasin tarihi ya zama farilla a makaranta

- Sanatan da yayi gwagwarmaya a zamanin Soja yace hakan na da amfani

Idan ba ku manta ba wannan Gwamnatin Shugaba ta kawo wasu tsare-tsare na yi wa tsarin ilmin Najeriya garambawul. Wani Sanatan Jam’iyyar APC mai mulki da ke wakiltar Jihar Kaduna yayi murna da daya daga cikin gyaran da aka kawo.

Dawo da darasin tarihi a makaranta zai taimakawa yara – Shehu Sani
Shehu Sani yace an kyauta da aka tilastawa Dalibai koyon tarihi

A cikin kokarin da Gwamnatin nan ta ke yi na gyara harkar ilmi an maida darasin tarihi ya zama tilas kan ‘Daliban kasar nan wanda Sanata Shehu Sani yake ganin lallai abu ne mai kyau Gwamnatin na tayi a wannan fanni da yake tabarbarewa.

KU KARANTA: Kwamitin Shehu Sani a Majalisa ya hana El-Rufai cin bashi

Sanata Shehu mai wakiltar Jihar Kaduna ta-tsakiya a Majalisar Dattawa yace dawo da darasin tarihi da aka yi a makarantun mu zai taimaka wajen ba yara masu tasowa madubin inda mu ka taso a kasar nan da kuma inda mu ka dosa a halin yanzu.

Sanatan ya kan yi amfani da shafin sadarwa na Tuwita ne ya tofa albarkacin bakin sa kan lamarin kasar. Kwamared Sani yayi magana game labarin da ake ji na damfarar Shugaba Buhari da aka yi da lambar yabon karya, yace sai a rika lura nan gaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng