Allah ya yiwa shakikin gwamna Masari rasuwa
Alhaji Isyaku Sulaiman, hakimin garin Masari dake karamar hukumar Kafur a jihar Katsina, ya rasu.
Marigayin dan uwa ne na kusa ga gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari.
Jam'iyyar PDP ta bakin sakatarenta na yada labarai, Alhaji Sani Garba da aka fi sani da 'Yellow', ta mika sakon ta'aziyya ga gwamna Masari.
A wata ganawa da ya yi da jaridar The Nation, Alhaji Sani, ya ce, mutuwar Alhaji Suleiman ta girgiza jam'iyyar PDP a jihar.
"Munji ciwon rashin dattijo a jihar Katsina. Ya mutu a daidai lokacin da ake bukatar aiyukan dattako irin nasa. Allah ya yi masa rahama," in ji Alhaj Sani.
Kafin rasuwar sa, Alhaji Isyaku Sulaiman; mai shekaru 84 a duniya, shine Madaki kuma hakimin garin Masari dake karamar hukumar Kafur.
DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kwace makamai 198 daga daga hannun makiyaya da barayin shanu a jihar Katsina
Ya mutu ya bar 'ya'ya da jikoki da dama, daga cikinsu akwai Alhaji Sani Isyaku Masari, babban sakatare a hukumar ma'aikatan jihar Katsina.
Tuni aka binne shi bisa tsarin addinin Islama a mahaifar sa, Masari.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng