Da Duminsa: 'Yan bindiga sun sake kai hari jihar Zamfara, sun kashe mutane da dama
A jiya, Talata, ne wasu 'yan bindiga suka kara kai hari kauyen Bawar Daji dake karamar hukumar Anka a jihar Zamfara tare da kashe mutane a kalla 12, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Mutanen kauyen sun shaidawa kamfanin jaridar Daily Trust cewar, 'yan bindigar, kimanin su 12 sun isa garin da misalin karfe 1:00 na rana suka harbe mutane kafin daga bisani su kara dawowa da misalin karfe 2:00 na dare inda suka kara kashe wasu mutane takwas.
Saidai hukumar 'yan sanda a jihar, ta bakin kakakinta, DSP Muhammad Shehu, ta ce mutane uku ne kawai suka mutu tare da tabbatar da afkuwar kai harin. Kazalika, ya ce, 'yan bindigar sun gudu ne bayan zuwan jami'an 'yan sanda.
Harin na zuwa ne cikin kasa da sati biyu bayan an harbe wasu mutanen takwas a kauyen Dogon Daji dake karamar hukumar Maru.
DUBA WANNAN: An kama dan leken asirin kungiyar Boko Haram a Kano
A farkon watan nan ne aka kashe gagararren shugaban masu tayar da hankula a jihar ta Zamfara da ake kira Buharin daji.
A wata tattaunawa da jaridar Daily Trust mazauna kauyukan dake karkashin karamar hukumar Anka, sun ce, wani mai suna Gajere ne ke jagorantar hare-haren da ake kaiwa kauyukan; Duhuwa, Dawan Jiya, Gobirawa, da Tungar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng