Mahaddaciyar Al-Qur’ani daga jihar Legas ta ciri tuta a jihar Katsina, an bata kyautar dalleliyar mota (Hoto)
An gudanar da gasar Al-Qur’ani na kasa daya gudana a jihar Katsina lafiya, an kuma kammala lafiya, sai dai wani abu da ya baiwa mahalartar gasar mamaki shine yadda wata dalibar Qur’ani bayarabiya ta yi fice a gasar.
Gasar wanda ta samu halartar kusan dukkanin jihohin Najeriya, itace ta karo 32, an fara shi ne tun daga ranar 23 ga watan Feburairu zuwa 3 ga watan Maris, inda aka taron kullewa.
KU KARANTA: Biki yayi biki: An kama Sanatocin Najeriya yayin da suke tikar rawa a bikin diyar Dangote
Wannan daliba data wakilci jihar Legas, na daga cikin zakakuran mahaddata da sukalashe gasar, inda ta sha gaban mahaddata da dama da suka fafata a wannan gasar Al-Qur’ani, tare da lashe babbar kyautar wata dalleliyar mota sabuwa fil, kirar Toyota 2018, kujerar Makkah tare da daukan nauyinta a karatu.
Hakazalika an samu wata hazikar data yi fice a nata fannin hadda da Tafsiri daga jihar Borno Malama Amina Aliyu, wanda ta samu kyautukan da suka hada da kujerar Makkah, Mota, N500,000, Jadduma, na’urar karanta Qur’ani da Kwamfuta.
Hakazalika daga jihar Sakkwato ne aka samu wadda ta mara mata Alaramma Amina baya, watua Zainab Aliyu Gidan Kanawa ta zamo ta biyu,
A bangaren maza kuma, wani Alaramma mai shekaru 20, Amir Yunus Quruu ne ya zamo zakaran gwajin dafi, wanda shi ma ya sam gwaggwaban kyautuka daga mashirya gasar. yayin da Aminu Bagarawa ya daga jihar Sakkwati ya zamo na uku, a haddar izu sittin da Tafsirinsa.
An gudanar da gasar ne a sansanin yan bautan kasa, NYSC dake Katsina, daga nan kuma aka gudanar da taron ranar karshe a babban filin wasanni na jihar Katsina, wato Muhammadu Dikko Stadium, inda gwamnatin jihar tace ta kashe naira miliyan 350 a shirye shiryen gasar daga farko har karshe.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng