Wuta tayi barna, ta kone daya daga cikin cibiyoyin bincike mafi amfani a arewacin Najeriya
Wata gobara da ta tashi yau Litinin, 26 ga watan Maris, 2018, ta kone daya daga cikin dakin binciken cututtuka mafi muhimmanci a nahiyar Afrika, dake garin Zaria a jihar Kaduna.
Cibiyar binciken kuturta, tarin shika, da kanjamau (NTBLC) na daga cikin cibiyoyin binciken kwakwaf a kan cututtuka dake dauke da kayan aiki da babu irinsu a cibiyoyin binciken cututtuka dake nahiyar Afrika.
Wakilin kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) da ya ziyarci wurin, ya ce wutar ta shafe fiye da sa'o'i uku tana ci kafin jami'an hukumar kashe gobara su shawo kanta.
Shugaban cibiyar binciken, Labaran Shehu, ya ki yin jawabi a kan faruwar lamarin bayan bayyana cewar, "har yanzu ba a san sababin tashin gobarar ba."
Kazalika, ya yi alkawarin cewar za a gudanar da binciken kwakwaf domin gano musabbabin gobara tare da sanar da manema labarai duk abinda ya kamata su sani.
DUBA WANNAN: Aure uku da suka girgiza Najeriya a watan nan
A wani labarin Legit.ng kun ji cewar, wata mata, Lauratu Abdullahi; mai shekaru 30, ta bukaci kotun shari'ar Musulunci dake magajin gari a Kaduna ta raba aurenta da mijinta saboda ya daina saduwa da ita tun bayan da cikinta ya girma.
Lauratu, ta shaidawa kotu cewar, mijinta, Yahaya Tanko, na yawan cin zarafinta duk da baya iya biyan bukatunta.
Ta sanar da kotun cewar mijinnata ya barta da yunwar abinci da kuma ta jima'i har na tsawon watanni hudu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng