Aure uku da suka girgiza Najeriya a watan nan
1. Fatima Ganduje Da Idris Ajimobi: An sha shagalin biki tsakanin diyar gwamnan jihar Kano, Fatima Abdullahi Ganduje, da dan gwamnan jihar Oyo, Idris Ajimobi.
An daura auren ranar 3 ga watan Maris a babban masallacin sallar juma'a na garin Kano dake fadar sarkin Kano, muhammadu Sanusi II. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya yiwa Idris walicci yayin da jagoran jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya kasance waliyyin amarya.
Bikin 'ya'yan gwamnonin ya sha suka a wurin 'yan Najeriya, musamman hotunan kafin biki da masoyan suka watsa a kafafen sada zumunta dake nuna ango, Idris, rungume da amaryarsa, Fatima, da hannunsa bisa kirjinta. Bayan an sha biki a Kano, an kuma shan wani shagalin a garin Ibadan, jihar Oyo, bayan an kai amarya dakin mijinta.
2. Fatima Dangote da Jamil Abubakar: Tun farkon shigowar shekarar nan ake yamadidi da maganar auren diyar attajiri Aliko Dangote, Fatima, da saurayinta da suka dade suna soyayya, Jamilu Abubakar; dan tsohon babban sifeton 'yan sanda, M.D Abubakar.
An daura auren ranar 16 ga watan Maris, 2018, a garin Kano, mahaifar Aliko Dangote.
Manyan attaijirai daga fadin duniya, masu mulki, sarakuna da masu fada a ji a gida Najeriya da kasashen ketare sun halarci shagalin bikin. An gudanar da shagalin biki a Otak din Eko dake garin Legas.
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari da manyan jami'an gwamnatin Najeriya, mai kudin duniya, Bill Gates, shugaban kasar Ghana, da ragowar masu kumbar susa daga fadin duniya sun halarci bikin.
3. Oluwadamilola Osinbajo da Oluseun Bakare: Oluwadamilola, babbar diyar mataimakin shugaban kasa, Farfesa Osinbajo, ta amarce da angonta, Oluseun Bakare, dan hamshakiyar biloniya 'yar kasuwa, Bola Shagaya.
An yi daurin auren gargajiya ranar alhamis, 15 ga watan Maris, kafin daga bisani a daura aurensu a coci ranar Asabar, 17 ga watan Maris, 2018.
Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo, ya yi kokari wajen takaita adadin jama'ar da zasu halarci shagalin bikin diyar ta sa tare da bayar da gargadi ga masu halartar bikin a kan wasa da kudi yayin bikin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng