Zargin kitsa satar ‘yan matan Dapchi: Bamu san saja Bako ba, bai taba aiki da mu ba – Hukumar soji

Zargin kitsa satar ‘yan matan Dapchi: Bamu san saja Bako ba, bai taba aiki da mu ba – Hukumar soji

Hukumar sojin Najeriya ta nesanta kanta daga wani rahoto dake yawo a dandalin Facebook da ragowar dandalin sada zumunta dake alakanta hukumar sojin da gwamnatin Najeriya da kitsa satar ‘yan matan Dapchi.

Wani mutum da ya kiran kansa Saja Bako ne ya fara watsa rahoton cewar, gwamnatin tarayya ce da hukumar sojin Najeriya suka kitsa sace ‘yan matan Dapchi a fadar gwamnati, kuma an kashe miliyan N80 domin tsara sace ‘yan matan da dawo da su.

A sanarwar da hukumar ta fitar ta bakin darektan yada labaranta, Birgediya Janar Texas Chukwu, ta ce bata san wani Saja Bako ba domin babu wani jami’inta mai wannan sunan har cikin wadanda suka yi ritaya.

Zargin kitsa satar ‘yan matan Dapchi: Bamu san saja Bako ba, bai taba aiki da mu ba – Hukumar soji
Tukur Buratai

Hukumar Sojin ta ce irin wadannan zargi marasa tushe ba baki bane a dandalin sada zumunta tare da yin kira ga jama’a das u guji alakanta hukumar da al’amuran siyasa.

Chukwu ya kara da cewa, binciken hukumar soji ya tabbatar da cewar an bude kafar da aka yi amfani da ita wajen watsa labaran, Dailyglobewatch.eu a ranar 14 ga watan Afrilu, 2017, kuma zai daina aiki ranar 14 ga watan Afrilu.

DUBA WANNAN: Mutane 6 sun mutu yayin kokarin gina dakin amarya a Sokoto

Hukumar sojin ta bayyana takaicinta bisa halayyar wasu mutane na yada karya domin cimma wata manufa y ta siyasa tare da yin kira ga jama’a das u yi watsi da irin wadannan maganganu tare da gargadin jam’a su guji yada duk wani zance da bai inganta ba.

Hukumar soji ta kara jaddada aniyarta ta yin aiki domin tabbatar da zaman lafiya da kuma nesantar da kanta daga duk al’amuran siyasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng