Barawon da ya sace biliyan 33 na yan fansho ya dawo da biliya 23 tare da fuskantar shekaru 6 a Kurkuku

Barawon da ya sace biliyan 33 na yan fansho ya dawo da biliya 23 tare da fuskantar shekaru 6 a Kurkuku

Wani tsohon jami’in gwamnatin Najeriya da ya wawushe kudin yan fansho na jami’an Yansandan Najeriya da suka yi ritaya, John Yusuf ya gamu da hukunci mai tsauri da ya dace da shi.

Legit.ng ta ruwaito kimanin shekaru biyar da suka gabata ne dai wata Kotu ta yanke ma John hukunci mai sassauci, sai dai hukumar EFCC ta dage sauraron karar zuwa Kotun daukaka kara dake babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Karfin hali barawo da sallama: Kotu ta yanke ma dalibin da yayi ma Sarkin Kano sojar gona

Hukuncin da kotun baya ta yanke ma John, wanda hukumar EFCC ke ganin hakan ba adalci bane, shi ne ta yanke masa hukucin zaman gidan Kurkuku na tsawon shekaru biyu ko kuma ya biya tara na naira dubu 750.

Barawon da ya sace biliyan 33 na yan fansho ya dawo da biliya 23 tare da fuskantar shekaru 6 a Kurkuku
John Yusuf

A zaman kotun na ranar Laraba 21 ga watan Maris ne Alkalan Kotun suka yanke ma barawon hukuncin daurin shekaru shidda a gidan Yari, tare da umartarsa da dawo da kudi naira biliyan 22.9.

Sai dai shima wand aake tuhuma John Yusuf ya amsa dukkanin tuhume tuhumen da ake yi masa, inda yace ya san dai ya wawushe naira biliyan 24 daga kudaden fansho na Yansandan Najeriya, don amfanin kashin kansa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng