Zamu kai wa jihar Kano harin bama-bamai - Barzanar wani tsohon soja ga matan Ganduje

Zamu kai wa jihar Kano harin bama-bamai - Barzanar wani tsohon soja ga matan Ganduje

- Rundunar SSS sun kama wani tsohon soja da yayi barazanar kai wa jihar Kano harin bama-bamai

- Matukar gwamna Ganduje bai zauna da mu ba za mu kai wa kasuwanni da makarantun cikin garin Kano hari inji tsohon soja da jami'an SSS suka kama

Jami’an rundunar tsaro ta SSS, sun kama wani tsohon Kaftin din soja mai ritaya a garin kano, bisa zargin yiwa uwargidan gwamna Abdullahi Ganduje, barazanar kai wa jihar Kano harin bama-bamai ta sakon text message da ya aika mata.

Tsohon sojan yayi barazanar kai wa kasuwanni da makarantu a garin Kano hari matukar gwaman jihar bai kira su, ya zauna da su ba.

Zamu kai wa jihar Kano harin bama-bamai - Barzanar wani tsohon soja ga matan Ganduje
Zamu kai wa jihar Kano harin bama-bamai - Barzanar wani tsohon soja ga matan Ganduje

Wani majiya mai karfi ya tabbatar da cewar uwargidan Ganduje ta aika da sakon zuwa wajen mijinta wanda shi kuma ya aika wa hukumar DSS.

KU KARANTA : Fusatattun matasa sun kona barawon waya a jihar Nasarawa

Tsohon Sojan, wanda aka kama shi a filin jirgin sama na, Aminu Kano, yace wani tsohon kwamishina a gwamnatin da ta gabata ne, ya sa shi aikin, kuma ya bashi naira miliyan N1,500,000 wanda aka samu a cikin asusun ajiyan bankin sa a lokacin da ake yi masa bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng