Bayan wasan bera na tsawon shekaru 10, hukumar DSS ta cafke shu'umin mai safarar bindigu
Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta ce ta yi nasarar cafke gagararren mai safarar bindigu, Jonah Abbey, da aka fi sani da Jonah Idi, tare da dirbansa, Agwo Saviour, da aka fi sani da Dan Wase.
Abbey, gagararren mai safarar bindigu, yana cikin jerin masu laifin da hukumar DSS ke nema ruwa a jallo tsawon shekaru 10 da su ka gabata.
Ana zarginsa da sayar da bindigu ga 'yan ta'adda a jihohin Najeriya da su ka hada da Bayelsa, Ebonyi, Ribas, Imo, Anambra, Filato, Nasarawa, da jihohin Taraba da Benuwe.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar yau, Lahadi, a Abuja, dauke da sa hannun Mista Tony Opuiyo, ta ce rahotannin sirri da hukumar ta samu sun tabbatar da cewar Abbey ya yi safarar wasu bindigu daga Konduga tab jihar Borno zuwa jihar Taraba ta hanyar amfani da direbansa, Saviour.
DUBA WANNAN: Dakarun soji sun samu gagarumar nasara a yaki da rikicin makiyay da manoma a jihar Benuwe
"Mai laifin ya dade yana safarar makamai, musamman bindigu, a jihohin Najeriya ta hanyar amfani da dilolinsa dake jihohin Filato, Ebonyi, Kuros Riba, Enugu, Bayelsa, da sauransu," a cewar sanarwar.
Sanarwar ta ce Abbey na samun samun bindigu daga kasar Kamaru da wasu jihohin kudu maso gabashin Najeriya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng