Majalisar Dinkin Duniya ta nada Aisha Buhari Jakada a Najeriya

Majalisar Dinkin Duniya ta nada Aisha Buhari Jakada a Najeriya

- Majalisar Dinkin Duniya ta sa Aisha Buhari wani babban baiki a Najeriya

- Matar Shugaban kasar za ta zama Jakadar UN na yaki da cutar kanjamau

- Hajiya Aisha Muhammadu Buhari tana da kokarin taimakawa yara a kasar

Mun samu labari cewa Uwargidar Shugaban Najeriya Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta samu wani mukami. Majalisar Dinkin Duniya dai ta nada Aisha Buhari ne a matsayin Jakadar UNAIDS a Najeriya.

Majalisar Dinkin Duniya ta nada Aisha Buhari Jakada a Najeriya
Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta zama jakadar yaki da Kanjamau

Aisha Buhari ta zama Jakadar musamman ta Majalisar Dinkin Duniya kan cutar kanjamau a Najeriya. Matar Shugaban kasar za tayi bakin kokari wajen ganin an rage samun yara da ke kamuwa da cutar wajen Mahaifan su.

KU KARANTA: Abin da Shugaba Buhari ya zanta da 'Yan Majalisa

Wani babban Jami’in yada labarai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya Mista Charles Martin-Jjuuko ya bayyana wannan jiya a Asabar a Abuja kamar yadda mu ka samu labari. Buhari za ta taimaka wajen rage yaduwar cutar sida.

Ana sa rai babban Darektan Majalisar na Dankin Duniya da ke lura da wannan bangare watau Micheal Sidibe zai aikowa Matar Shugaban Kasar takarda a Ranar Litinin. Wata gidauniya ta Matar Shugaban kasar ta sanar da wannan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel