Sauya sheka: Mutane fiye da 2000 sun bar APC zuwa PDP a jihar Kano

Sauya sheka: Mutane fiye da 2000 sun bar APC zuwa PDP a jihar Kano

- Fiye da mutane 2000 ne suka sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP a jihar Kano

- Wandanda suka sauya shekan sun ce ana nuna musu wariyya da banbanci ne shiyasa suke fice daga jam'iyyar

- Wandanda suka sauya shekar sun zargi mai bawa shugaba Buhari shawara kan ayyukan Majalisar kasa da yin babakere cikin harkokin jam'iyyar a karamar hukumar Sumaila

A ranar Litinin, 13 ga watan Maris, sama da mutane 2000 ne suka sauya sheka daga jam'iyyar mai mulki ta APC zuwa jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Kano.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa wannan gagarumin sauyin shekar ya faru ne a karamar hukumar Sumaila da ke jihar Kano.

Mutane 2000 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP a jihar Kano
Mutane 2000 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP a jihar Kano

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau, Aminu Wali da kuma Gambo Salau ne suka karbi mambobin da suka sauya sheka zuwa PDP.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari na tsoron shan kaye - Jam'iyyar UPP

Wanda ya jagoranci wadanda suka sauya shekar, Surajo Kanawa, ya yi ikirarin cewa mai bawa shugaba Buhari shawara kan harkokin da suka shafi Majalisar Kasa, Abdulrahman Sumaila ne yayi babakere kan harkokin jam'iyyar a karamar hukumar Sumaila.

A cewarsa, Sumaila ya mayar da su saniyan ware kuma baya wata harkan arziki tare da su kawai sai dai yan korar sa ya ke harka dasu. Yayi ikirarin cewa ba'ayi musu adalci a jam'iyyar kuma an toshe duk wata kafa da zasu yi amfani dashi wajen kai kara zuwa hedkwatan jam'iyyar.

A wani rahoton, Legit.ng ta ruwaito muku cewa tsohon shugaban riko na jam'iyyar PDP, Ahmed Makarfi ya bayyana cewa wasu 'ya'yan jam'iyyar za su fice daga jam'iyyar.

Makarfi yayi wannan hasashen ne bayan ficewar wasu kusoshi daga jam'iyyar wanda suka hada da Jerry Gana, Tunde Adeniran da ma wasu zuwa jam'iyyar SDP.

Duk da haka, ya ce ba wani abin damuwa bane kamar yadda wasu kafafen yadda labarai ke ruruta labarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164