Barayi sun farwa ma'aikatan NNPC sun gudu da miliyan 16 a Kano

Barayi sun farwa ma'aikatan NNPC sun gudu da miliyan 16 a Kano

- Matsalar fashi da makami dai ba yau aka fara ta ba a Najeriya

- Matsalar ta zama ruwan dare, inda barayi zasu tare mutum, ko su shiga gidan shi, suyi mashi sata. wasu ma har kashewa suke yi idan basu samu abinda suke so ba.

- A jiya ne barayi suka kwace kudi kimanin naira milyan 16 a jihar Kano, wanda wasu ma'aikatan NNPC suke kokarin kaiwa banki a jiya

Barayi sun farwa ma'aikatan NNPC sun gudu da miliyan 16 a Kano
Barayi sun farwa ma'aikatan NNPC sun gudu da miliyan 16 a Kano

A ranar litinin dinnan ne wasu da ake zargin barayi ne suka farwa ma'aikatan NNPC dake unguwar Hotoro a Kano, inda suka arce da miliyan 16.

Wani shaida ya tabbatar wa da manema labarai cewa barayin sun zo su ne da misalin karfe 8 na safe, a dai dai lokacin da ma'aikatan suke shirin hada kan kudin domin kaiwa banki. Ya ce barayin sun far musu ne, inda suka kwace jaka daya wacce ke dauke da kudi kimanin naira miliyan 16, ya ce bayan barayin sun kwace jakar sai suka fara harbin iska domin su tsorata mutanen dake wurin suka kuma arce da kudin.

DUBA WANNAN: Birane 50 mafi hatsari a duniya

Da aka tuntubi jami'in 'yan sanda na jihar SP Magaji Musa Majiya, ya tabbatar da faruwan abun, inda ya ce, abin ya faru ne a dai dai Kwanar Mashaya lokacin da motar ma'aikatan take shirin shan kwana, sai ga barayin sun zo su biyu, suka warce jaka daya daga cikin jakankunan, kuma suka gudu.

Sannan kuma ya ce hukumar 'yan sanda ta kama ma'aikatan NNPC din su uku wanda ake zargin suna da hannu a satar, sannan ya kara da cewar, kudin da aka sace din na cinikin da aka yi ranar Juma'a, Asabar, da kuma Lahadi ne. Ya kuma kara da cewa suna nan suna yin iya bakin kokarin su wurin ganin sun kamo wadanda suka gudu da kudin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng