Kashedin Juyin Mulki?: Sojin Najeriya sun tsawatar kan yawan kashe-kashe a jihohin Najeriya

Kashedin Juyin Mulki?: Sojin Najeriya sun tsawatar kan yawan kashe-kashe a jihohin Najeriya

- Ana samun juyin mulki ne yayin da aka sami tabarbarewar tsaro a kasa

- Najeriya ta dade bata ga juyin mulki ba a shekarun nan

- Sojin Najeriya sun saki kashedi ga 'yan siyasa da 'yan Najeriya

Juyin Mulki: Sojin Najeriya sun tsawatar kan yawan kashe-kashe a jihohin Najeriya
Juyin Mulki: Sojin Najeriya sun tsawatar kan yawan kashe-kashe a jihohin Najeriya

Sabuwar sanarwa daga hukumar sojin kasar Najeriya, a shafinta na sadarwar zamani ta facebook, ta tsawatar da kashedi cikin bababar murya, kan yawan kashe-kashe dake faruwa a jihohin kasar nan, musamman a cewarta, jihohin Adamawa, Taraba da Binuwai.

A sanarwar, wadda ta fitar awa hudu da suka wuce da yammacin yau dinnan lahadi, hukumar tayi tir da Allah-wadai da wadannan munanan kashe-kashe, wadanda ta kira na rashin hankali.

Hukumar ta tsawatar ga masu tayar da zaune tsaye, da cewa idon hukumar yana kansu, inda tace ita da sauran hukumomi kawayenta na tsaro suna biye da duk wani abu dake faruwa na tu'annati a fadin kasar nan.

Sanarwar, wadda ta fito ta hannun Birgediya Janar Texas Chukwu, jami'in sadarwar Sojin Kasar Najeriya, tace sojin zasu sanya kafar wando ga duk masu son tayar da fitina a jihohin kasar nan, sannan kuma zasu kamo duk wadanda ke daukar nauyin wadannan barna.

DUBA WANNAN: Kwanan nan za'a dankarawa taba da giya tsada a Najeriya

Sanarwar, ta kuma ce, hukumar tsaro ta sojin, tana kan aikinta na tabbatar da tsaro a inda ake tarzoma, kuma tana bin dukkan ka'kidojin aiki kamar yadda dokar kasa da ta duniya ta tanada.

A baya dai, akwai gutsuri-tsoman cewar sojin najeriya na iya juyin mulki saboda matsalolin tsaro a kasar nan, amo wanda mataimakin shugaban majalisar kasar nan Ike Ikweremadu ya amsa kuma ya iyar da babbar murya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng