Masu garkuwa da mutane, barayin shanu da yan fashi da makami 50 sun fada komar Yansanda a Katsina
Rundunar Yansandan jihar Katsina, dake yankin Arewa maso yammacin Najeriya, ta sanar da samun wata gagarumar nasara a aikinta bayan ta kwato bindigu guda 12 daga hannun miyagun mutane.
Kwamishinan Yansandan jihar, Muhammad Wakili ne ya sanar da haka a yayin ganawa da manema labaru a shelkwatar Yansandan jihar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito shi.
KU KARANTA: Wani dan majalisa ya wancakalar da kujerarsa don nuna ɓacin rai game da hamɓarar da gwamnatin Mugabe
Kwamishinan Mohammed yace daga watan Janairu zuwa Feburairu 2018 sun kama yan fashi da makami, masu garkuwa da mutane da kuma barayin shanu har guda hamsin, inda a suka kwato bindigu 12 daga wajensu.
Daga cikin bindigun akwai AK 47 guda hudu, kananan bindigu guda takwas da alburusai da dama, kamar yadda kwamishinan ya shaida ma majiyar Legit.ng, ya kara da cewa sun samu nasarorin nan ne a sakamakon hadin gwiwa da kyakkyawar alaka dake tsakaninsu da al’umman gari masu basu bayanan sirri.
Zuwa yanzu jami’an yansanda na cigaba da gudanar da bincike bincike kan mutanen da aka kama, kuma za’a gurfanar da su gaban Kotu da zarar an kammala bincike binciken.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng