Kasar Thailand ta zargi shugaba Buhari da laifin rushewar Kamfanonin Shinkafa na Najeriya

Kasar Thailand ta zargi shugaba Buhari da laifin rushewar Kamfanonin Shinkafa na Najeriya

Ministan noma da raya karkara, Mista Audu Ogbeh, ya bayyana cewa kasar Thailand ta na zargin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, wajen taka rawar gani na rushewar manyan kamfanoni 7 na shinkafa a kasar nan.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne ministan ya bayyana hakan, a yayin taron kungiyar manoma da kuma takin zamani da aka gudanar a farfajiyar zaman majalisa ta fadar shugaban kasa dake babban birni na tarayya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Legit.ng ta fahimci cewa, shugaba Buhari shine ya jagoranci wannan taro kamar yadda Kamfanin Dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.

Ministan yake cewa, Jakadan kasar Thailand zuwa Najeriya shine ya yi wannan zargi a yayin da ya ziyarce shi tun a watan Fabrairun da ya gabata.

KARANTA KUMA: An dakatar da ma'aikatan lafiya 4 da laifin bude kwakwalwar wani mara lafiya bisa kuskure

A cewar Ministan, Jakadan ya yi korafi akan rushewar kamfanonin shinkafa da a yanzu ya haddasa koma baya na rashin aikin yi a kasar nan, wanda barazana ce ga tattalin arziki.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a ranar Alhamis din da ta gabata ne wata 'Yar Kunar Bakin Wake ta tayar da bam a masallacin Buni-Yadi dake birnin Damaturu na jihar Yobe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel