Firdausi Amasa: Kotu ta hana ‘Yan Majalisa zama game da batun Hijabi
- An hana ‘Yan Majalisa zama game da rikicin amfani da Hijabi a Najeriya
- Majalisar Wakilai ta so a gayyaci Jama’a a zauna domin tattauna batun
- An hana Firdausi Amasa shaidar koyon harkar shari’a saboda ta sa Hijabi
Dazu mu ka ji cewa Kotu ta haramtawa Majalisa sa baki a maganar Firdausi Amasa wanda aka hana ta shaidar koyon ilmin shari’a a dalilin rashin cire hijabi da tayi kwanakin baya.
Jaridar Punch ta rahoto cewa Kotun Tarayya da ke Abuja ta zauna inda ta hana ‘Yan Majalisa Wakilai sa baki game da batun Firdausi Amasa. A baya Majalisa ta shirya zama na musamman har aka gayyaci Jama’a domin wannan magana.
KU KARANTA: An sace matar wani babban 'Dan jarida a Kaduna
Alkali mai shari’a Anwuli Chikere ta yanke wannan hukunci bayan da wasu Lauyoyi su ka shigar da kara inda su ke nemi a dakatar da Majalisar Kasar game da yunkurin ta na zama kan batun. Alkalin ta nemi a dakata yanzu har sai an gama kara.
Yanzu dai an dage shari’ar har sai karshen Watan Afrilu inda ake sa rai za a cigaba da karar. Yanzu dai Majalisar Wakilai za ta jira har sai wannan lokacin kafin ta dauki matakin da ta yi niyya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng