Ya kamata Gwamnoni su daina gantalin zuwa fadar Shugaban kasa bini-bini – Shehu Sani
- Sanata Shehu Sani yayi tir da Gwamnonin da ke gantali a Abuja
- ‘Dan Majalisar yace dole Gwamnoni su tsaya su kare Jama’ar su
- A cewar Sanatan Kasar Gwamnonin na sabunta mubaya’ar su ne
A kwanan nan ne wani fitaccen Sanata daga Jihar Kaduna yayi tir da abin da wasu Gwamnonin Jihohin kasar nan ke yi na zuwa ziyarar Shugaban kasa Buhari bini-bini yayin da ake barna a Jihohin su ta shafin sa na Tuwita.
Sanata Shehu Sani yace dole a kawo karshen wannan sabuwar al’adar da aka kirkiko a lokacin mulkin Shugaba Buhari da Gwamnoni ba su da aiki sai zuwa ganin Shugaban kasa a fadar sa yayin da ake ta’asa a cikin Jihohin su.
KU KARANTA: Kashe-kashen Jihar Zamfara na neman ya fi karfin Jami’an tsaro
Kwamared Shehu Sani yace Gwamnonin na zuwa fadar Shugaban kasar ne domin jaddada mubaya’ar su a kai- a kai. A sanadiyyar wannan dai Sanatan Kasar yace wani lokaci ake barin tsaron daukacin mutanen Gari a hannun Allah.
Kwanan nan wasu ‘yan bindiga sun kashe dinbin mutane a Garin Birane a Jihar Zamfara. Sanatan yace Duniya ta fi damuwa da kashe-kashen da ya auku a Garin Florida a Kasar Amurka a kan wannan mummunan hari saboda makirci.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng