Suruki na ya cancanci ya rike Jihar Imo - Inji Gwamna Okorocha
- Gwamnan Jihar Imo Okorocha yace surukin sa ya cancanci ya gaje shi
- Gwamna Rochas Okorocha yace Uche Nwosu matashi ne mai jini a jika
- Nwosu yana auren diyar Okorocha kuma yana cikin manya a Gwamnati
Mun samu labari cewa Gwamna Rochas Okorocha ya bayyana cewa Surukin sa watau Uche Nwosu da ke auren babban diyar sa ya cancanci ya rike Gwaman Jihar Imo bayan sa yayin da shi yake shirin barin kujerar sa a 2019.
Mai Girma Gwamna Okorocha na Jihar Imo ya bayyanawa manyan 'Yan Jam'iyyar ta su ta APC daga Yankin Owerri wannan ne bayan da su ka kai masa ziyara a ofishin sa a Ranar Litinin. Gwamnan ya yabawa surukin na sa.
KU KARANTA: APC ta shiga rudani har abu ya kai ga zanga-zanga
A cewar Gwanna Rochas Okorocha ta bakin babban Sakataren sa na yada labarai surukin na sa zai dace da Gwamnan Jihar inda yace mutum ne matashi mai himma kuma ba shi girman kai don haka mulki ba zai taba canza ba.
Rochas Okorocha yace Nwosu mutum ne da ba ya nuna bambanci kuma ba ya shiga rikici da Jama'a duk da matsayin sa na shugaban Maikatan gidan Gwamnati. Gwamnan yace idan Nwosu zai fito takara, to zai goya masa baya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng