Cikin Hotuna: Jaruman Kannywood sun karrama shugaban tace fina-finai a jihar Kano
A sakamakon yaba wa da karamcin da gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ke yiwa jaruman shirya fina-finan hausa na kannywood, kungiyar jaruman ta karrama wani shugaban hukumar tace fina-finai na jihar.
Legit.ng ta fahimci cewa, kungiyar jaruman kannywood karkashin jagorancin Alhassan Kwalli, ta karrama shugaban tace fina-finai da dabi'u na jihar Kano, Mallam Ismail Na'abba Afakallah
KARANTA KUMA: Yadda za a kawo ƙarshen wahalar man fetur a ƙasar nan - Dogara
Shafin jaridar Rariya ya ruwaito cewa, baya ga Alhassan Kwalli, sauran shahararrun jaruman da suka halarci taron karamcin sun hadar da; Ali Nuhu, Nura Hussain, Isa A. Isa, Lawal Ahmad, Baba Karami da sauransu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng