Wani Matashi ya ba Mata kayan koyon aiki da jarin kasuwanci a Katsina

Wani Matashi ya ba Mata kayan koyon aiki da jarin kasuwanci a Katsina

- Wani Matashi da yayi karatu ya bude gidauniya a Garin Matazu

- Hamzah Ukashatu ya rabawa mata akalla 300 kayan koyon sana’a

- Wannan kwararre ya kuma rabawa yara da marayu kayan karatu

Mun samu labari cewa Wani Matashi da yayi karatu ya rika a Jihar Katsina mai suna Hamzah Ukashatu Musa ya ba dinbin Mata masu karamin karfi kayan koyon sana’a da kuma jari na kasuwanci a Garin Matazu a karshen makon nan.

Wani Matashi ya ba Mata kayan koyon aiki da jarin kasuwanci a Katsina
Hamzah Ukashatu ya rabawa Mata kayan koyon sana'a

Hamzah Matazu ya kafa wata gidauniya ne mai suna Gidauniyar Ukashatu wanda ta shirya tallafi na musamman ga mata 300 masu kananan sana’o’i irin su kosai, awara, da kuli-kuli. Bayan nan an kuma hada injin taliya 50 ga mata masu sana’a.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje ya nada wasu sababbin mukamai

Wani Matashi ya ba Mata kayan koyon aiki da jarin kasuwanci a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina ya halarci wannan taro a Matazu

Gidauniyar ta kuma samawa ‘yan makaranta kayan karatu da su ka hada da litattafai da tebura da kujeru 50 da jakkuna ga mata 100 masu zuwa Islamiyya. Haka kuma Gidauniyar ta hada har da kayan makaranta ga marayu 100 na Firamare.

Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina ya halarci wannan taro da aka yi inda har ya bada gudumuwar Naira Miliyan ga gidauniyar. Manyan Gwamnati da ‘Yan APC na Jihar Katsina sun halarci wannan taro inda wannan kwararren matashi ya raba kayan alheri.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng