Yanzu-yanzu: Mun kara albashin malaman makarantun gwamnati da kashi 27.5% - Gwamnatin jihar Kaduna
Gwamnatin jihar Kaduna a yau Alhamis ya alanta cewa ta kara albashin malaman makarantun gwamnati da kasha 32.5 cikin 100.
Kwamishanan ilimi, kimiya da fasahan jihar Kaduna, Ja’afaru Sani, ya bayyana wannan ne a wata hira da manema labarai a Kaduna inda yace za’a karawa dukkan malaman makarantu kasha 27.5, sannan Karin kasha 5 ga malaman da zasu karantar a kauyuka.
Game da cewarsa, za’a baiwa mudirai masauki mai dakuna 3, sannan sauran malami dakuna 2 kari da Babura da za’a basu domin saukaka tafiyarsu zuwa makaranta.
Game da cewarsa, hakan ya zama wajibi domin tabbatar da zaman kwararrun malamai a karkara.
“A yanzu haka, malamai sun fi yawa a birane sabanin karkara, kuma hakan ya faru ne saboda albashinsu daya ne saboda haka, idan aka tura malamai kauyuka suna komawa birane.”
KU KARANTA: Sabuwar kungiyar Obasanjo ba ta bamu tsoro - APC
Sani yace za’a tura sabbin malaman da za’a dauka 10,000 makarantun firamare makonni 2 masu zuwa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng