Nau'o'in Abinci guda 7 da su ke taimako wurin narkewar abinci

Ko kun san cewa akwai wasu kalolin abinci wadanda su ke taimakawa wurin narkewar abinci? Ga uwa uba karin lafiya da kuma rigakafin cututtuka da su ke yi.

Ba su tsaya ga nan ba, hatta nutsuwa da kuzari da kuma samun barci mai dadi duk su na yi

Albishirin ku, Legit.ng ta samu zakulo maku bayanai daga rubutun da kamfanin dillancin abinci na Jumia ta yi na game da irin gudummuwan da wadannan abinci su ke bayarwa.

1) MADARAR YOGOT

Nau'o'in Abinci guda 7 da su ke taimako wurin narkewar abinci

Nau'o'in Abinci guda 7 da su ke taimako wurin narkewar abinci

Madarar yogot na dauke da kwayoyin bakteriya da su ke taimakawa wurin narkar da abinci. Shan sa ya na karawa ciki lafiya kuma ya na kare sa daga gudawa da kuma ciwon daji.

2) GWANDA

Nau'o'in Abinci guda 7 da su ke taimako wurin narkewar abinci

Nau'o'in Abinci guda 7 da su ke taimako wurin narkewar abinci

Gwanda ya na dauke da bitamin A da B da C, wadanda su ke fitar da cuta daga jiki. Shan gwanda kimanin awa 1 bayan cin abinci ya na taimakawa narkewar sa.

3) AYABA

Nau'o'in Abinci guda 7 da su ke taimako wurin narkewar abinci

Nau'o'in Abinci guda 7 da su ke taimako wurin narkewar abinci

Cin ayaba ya na kara lafiyar ciki. Ya na kuma taimakawa narkewar abinci masu gina jiki.

KU KARANTA: 'Yan a ware na PDP sunyi sulhu da uwar Jam'iyyar

4) KIFI

Nau'o'in Abinci guda 7 da su ke taimako wurin narkewar abinci

Nau'o'in Abinci guda 7 da su ke taimako wurin narkewar abinci

Kifi na dauke da sinadarin da ke hana kumburin ciki. Ya na kara lafiyar ciki da kuma narkewar abinci.

5) WAKE

Nau'o'in Abinci guda 7 da su ke taimako wurin narkewar abinci

Nau'o'in Abinci guda 7 da su ke taimako wurin narkewar abinci

Wake ya na saukake sulalewar abinci a cikin ciki. A ci wake a sannu idan ya na bata ciki.

6) DANKALIN HAUSA

Nau'o'in Abinci guda 7 da su ke taimako wurin narkewar abinci

Nau'o'in Abinci guda 7 da su ke taimako wurin narkewar abinci
Source: Twitter

Dankalin hausa ya na dauke da sinadarai da su ke saukaka narkewar abinci. Ya na kuma kara lafiyar ciki.

7) TUFFA (APPLE)

Nau'o'in Abinci guda 7 da su ke taimako wurin narkewar abinci

Nau'o'in Abinci guda 7 da su ke taimako wurin narkewar abinci

Apple na dauke da miniral da bitamins da dama wadanda su ke saukaka narkewar abinci. Ya na kuma dauke da sinadaran da su ke hana lalacewa da kumburin ciki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel