Gwamnati ta yi rusau a gidan Uwargidar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

Gwamnati ta yi rusau a gidan Uwargidar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

Uwargidar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Patience Jonathan na cigaba da fuskantar azal daga gwamnati, inda aka ruguza wani katafaren gidanta dake garin Abuja a ranar Talata.

Prmium Times ta ruwaito hukumar kula da gine gine a garin Abuja ne ta gudanar da wannan aikin rusau a kan gidan, wanda ke kan titin Shehu Musa Yar’adua a unguwar Kado, sakamakon an gina shine ba’a kan ka’ida ba.

KU KARANTA: Kungiyoyin Musulmai sun gwabza a kan lokacin Sallar juma’a, mutum 1 ya mutu

Sai dai wani lauya Emmanuel Anene ya shaida ma kamfanin dillancin labaru cewa yayi mamakin yadda hukumar ta rusa gidan, duk da cewar maganan na gaban kotu,kuma ba’a kammala sauraron shari’ar ba.

Gwamnati ta yi rusau a gidan Uwargidar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

Gidan Uwargidar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

Majiyar Legit.ng ta ruwaito lauyan yana fadin: “Jami’an hukumar sun taba zuwa a baya suna zargin ginin bashi da takardar izini, amma mu ka nuna musu takardun izinin gina gidan, kuma sun nuna mana sun gamsu da sahihancin takardun, don haka mun dauka maganar ta mutu.

“Don haka nayi matukar mamakin yadda tsakar rana kawai suka fara rusa gidan, kuma basu sanar damu zasu zo ba.”

Dayake mayar da martini, Daraktan hukumar, Muktar Usman ya tabbatar ma majiyarmu cewa ginin ba shi da izini, kuma sun aika musu da sanarwar rushewa, sa’annan yace wasu mutane a gidan ma sun yi ma wasu jami’ansu dukan tsiya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel