Neman miji: Ko yau na samu miji da gudu zan yi aure - Rashida mai sa'a
- Tsohuwar jarumar Kannywood ta bayyana irin wahala da suke sha wajen samun mazajen aure
- Rashida ta sha alwashin yin aure da zarar ta samu aure
- A halin da ake ciki jarumar na rike da mukamin mai ba gwamnan jihar Kano shawara
Fitacciyar tsohuwar jarumar nan ta dandalin shirya fina-finan Kannywood kuma 'yar siyasa, Rashida Adamu wacce aka fi sani da Rashida mai sa'a ta jadadda cewa suna matukar shan wuya yanzu wajen samun mazajen aure.
Jarumar ta bayyana hakan ne a 'yan kwanakin nan kamar dai yadda majiyarmu ta ruwaito, ta sha alwashin cewa a duk lokacin da ta samu manemi, babu shakka da gudu zata aure shi.
KU KARANTA KUMA: Labari mai dadi: Mahaddata Al-Qur'ani mai tsarki na kara yawa a kasashen Turai
Koda yake dai a yanzu jarumar tuni ta daina fitowa a cikin fina-finai sannan kuma ta tsunduma cikin harkokin siyasa inda daga baya gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya nada ta a matsayin mai ba shi shawara.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng