Fina-finan Hausa da su ka ratsa gari a shekarar bara

Fina-finan Hausa da su ka ratsa gari a shekarar bara

- Mun dauko fina-finan da su kayi tashe a shekarar bara

- Daga cikin su dai akwai fim din Rahma Sadau na Rariya

- Fim din Mijin Yarinya ne wanda aka fi maganar sa a 2017

Mun kawo maku jerin wasu manyan fina-finan wasan Hausa da su kayi tashe a shekarar da ta gabata. Jaridar nan ta Premium Times ne dai tayi aikin kawo wadannan fina-finai. Ga su kuma kamar haka:

1. Mijin Yarinya

Wannan fim da Ali Gumzah ya shirya yayi fice a 2017 na wata sabuwar ‘Yar wasa wanda aka auro a fim din, ta kai saboda tsabar so da Mai gidan yake yi mata abin har ya zama kamar hauka.

Fina-finan Hausa da su ka ratsa gari a shekarar bara
Sadau ta fito a cikin manyan fina-finan Kannywood

2. Rariya

‘Yar wasar da aka sallama daga Kannywood kwanaki watau Rahma Sadau ce da wannan aiki inda ta nuna yadda ake soyayya tsakanin yaran manya da kuma Talakawa a wani fim din ta.

KU KARANTA: An gano gidan da ake ketawa Mata hakki a Arewa

3. Mansoor

Manyan ‘Yan wasa da dama irin su Ali Nuhu, Babale Hayattu, Sadiq Ahmad da kuma Umar Shareef ne su ka fito a wannan fim da aka buga soyayya na kin-karawa.

4. Auren Manga

Auren Manga dai ya kayatar inda manyan ‘Yan wasa irin su Bosho, Adam Zango da Hadiza Gabon su ka nuna kwarewar su a a ciki.

5. Kanwar Dubarudu

A wannan fim dai an nuna Ali Nuhu da Rahma Sadau sun tashi a matsayin ‘Yan uwa masu kaunar juna. An nuna barkwanci kwarai a fim din.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng