'Yan tawaye sun kai wa Sojoji hari a Kamaru

'Yan tawaye sun kai wa Sojoji hari a Kamaru

Rahotanni daga rundunar tsaron kasar Kamaru sun bayyana cewa wasu yan ta’adda sun kai farmaki kan wani kauye inda suka farwa jami’an sojoji na kasar.

A cewar rundunar tsaron a daren ranar Alhamis, 14 ga watan Disamba ne ‘yan ta’addan suka kai hari kauye da ke samun kulawar sojoji sakamakon ayyukan ta’addanci da ke ta’azzara.

Ko da ya ke babu tabbacin wadanda suka kai harin amma akwai kyakkyawan tsammanin ‘yan ta’addan sun fito ne daga yankin da ke amfani da yaren Ingilishi la’akari da yadda su ke kai makamantan farmakin kan bukatarsu ta ganin an fitar da su daga Kamaru.

'Yan tawaye sun kai wa Sojoji hari a Kamaru
'Yan tawaye sun kai wa Sojoji hari a Kamaru

KU KARANTA KUMA: Kotu ta ba gwamnatin tarayya umurnin kwace gidaje 4 da motocin alfarma 86 na wani ma’aikacin gwamnati

Ma’aikatar yada labaran kasar ta ruwaito cewar sun yi awon gaba da manyan bindigogi 26 da kananan bindigu da wayoyin salula 20 sai kuma riguna masu tambarin jami’an tsaron yankin mai amfani da yaren Ingilishi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng